Bola Tinubu Ya Taya Gwamnan PDP Murnar Samun Nasara a Kotu, Ya Ba Shi Wata Muhimmiyar Shawara
- Zaɓaɓɓen shugaban ƙasa, Bola Tinubu, ya taya gwamna Ademola Adeleke na jihar Osun, murnar nasarar da ya samu a kotun ƙoli
- Tinubu ya kuma yabawa Gboyega Oyetola bisa ƙara ƙarfafa dimokuraɗiyya a ƙasar nan, ta hanyar neman ƴancin sa, har zuwa gaban kotun ƙoli
- Daga nan, ya buƙaci gwamnan na jihar Osun da ya natsu ya fara aiki sannan ya haɗa kan mutanen jihar
FCT, Abuja - Bola Tinubu, zaɓaɓɓen shugaban ƙasa, ya aike da saƙon taya murnar sa ga Ademola Adeleke, gwamnan jihar Osun, ƙan nasarar da ya samu a kotun ƙoli a ranar Talata, 9 ga watan Mayun 2023.
Tinubu, a wata sanarwa da ya aikewa da Legit.ng, wacce hadimin sa Tunde Rahman ya rattaɓawa hannu, ya buƙaci gwamnan da ya yi ƙoƙarin haɗa kan al'ummar jihar da gaggawa.
Zaɓaɓɓen shugaban ƙasar, ya ce kotun ƙoli ta kawo ƙarshen tirka-tirkar da ta fara tun daga kan zaɓen gwamnan jihar na watan Yulin 2022, inda ya ƙara da cewa dole ne kowane ɓangare ya mutunta hukuncin kotun ƙolin.
Tinubu ya kuma yabawa gwamnan jihar wanda ya sauka, Gboyega Oyetola, bisa yadda ya sauke nauyin da ke kan sa cikin aminci a lokacin mulkin sa na farko a matsayin gwamnan jihar.
DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar
Ya bayyana cewa tsohon gwamnan ya ƙara ƙarfafa dimokuraɗiyyar ƙasar nan, ta hanyar da ya nemi haƙƙin sa cikin kwanciyar hankali tun daga farko har zuwa ƙarshe.
Wani ɓangare na sanarwar na cewa:
"Yanzu da maganar zaɓen gwamnan jihar Osun na ranar 16 ga watan Yulin 2022, ta kawo ƙarshe, ina roƙon gwamna Adeleke da cikin gaggawa ya natsu cikin ya fara aiki, sannan ya cigaba daga inda tsohon gwamna ya tsaya."
Zaɓen Shugaban Kasa: Atiku Ya Ɗauki Manyan Lauyoyi 19 Don Kwace Nasara Daga Hannun Tinubu A Kotu, Jerin Sunaye
"Yanzu kamata ya yi ya haɗa kan jihar. Haka kuma ina roƙon dukkanin mutanen jihar da su yi aiki tare domim zama lafiya da cigaba a jihar."
Gwamnan Adeleke Ya Yi Magana Kan Nasarar Sa a Kotu
A wani labarin na daban kuma, gwamna Ademola Adeleke, ya sadaukar da nasarar da ya samu a kotun ƙoli zuwa ga ubangiji.
Adeleke ya kuma nemi abokin hamayyar sa Gboyega Oyetola da jam'iyyar APC su zo a haɗa hannu tare domin ciyar da jihar.gaɓa.
Asali: Legit.ng