Majalisa Ta 10: Manyan Dalilai 2 Da Suka Sanya Bola Tinubu Goyon Bayan Akpabio

Majalisa Ta 10: Manyan Dalilai 2 Da Suka Sanya Bola Tinubu Goyon Bayan Akpabio

  • Jam'iyya mai mulki ta APC ta kai kujerar shugaban majalisar dattawa yankin Kudu maso Kudu, sannan ta sanar da Godswill Akpabio a matsayin ɗan takararta
  • Zaɓar da aka yiwa Akpabio ya ba masana harkokin siyasa mamaki, waɗanda suka yi zaton za a kai kujerar yankin Kudu maso Gabas
  • Sai dai, zaɓin da Tinubu ya yiwa Akpabio na da alaƙa mai ƙarfi da dalilan tattalin arziƙi da siyasa

Abuja - Jam'iyyar All Progressives Congress (APC) mai mulki, ta sanar da kai kujerar shugabancin majalisar dattawa yankin Kudu maso Kudu, sannan ta zaɓi Godswill Akpabio, a matsayin ɗan takarar da ta ke marawa baya.

Felix Morka, kakakin jam'iyyar APC na ƙasa, a wata sanarwa ranar Litinin, ya ce kwamitin gudanarwa na ƙasa (NWC) na jam'iyyar ya cimma matsayar ne, bayan tattaunawa da zaɓaɓɓen shugaban ƙasa, Bola Tinubu, da wasu sauran manyan ƙusoshi.

Kara karanta wannan

Tinubu, Atiku Da Obi: Abubuwa 5 Da Suka Wakana Yau A Kotun Sauraron Ƙarar Zaɓe

Manyan dalilan Tinubu na goyon bayan Akpabio
Manyan dalilan goyon bayan Tinubu ga Akpabio sun bayyana Hoto: Bola Tinubu
Asali: Twitter

Zaɓin na Akpabio na da alaƙa da garaɓasar da Tinubu zai kwasa ta fannin siyasa da tattalin arziƙi, fiye da sauran ƴan takarar da ke neman kujerar da suka fito daga yankin Kudu maso Gabas.

1. Dalilin siyasa

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Akpabio shine ɗan takarar shugaban ƙasa na farko da ya fara janyewa Bola Tinubu, a lokacin zaɓen fidda gwani na shugaban ƙasa na jam'iyyar APC, inda ya bayyana shi a matsayin mutum mai kaifin hangen nesa.

Tsohon ministan ba wai kawai ya nuna goyon bayan sa ga Tinubu ba ne, sai da ya tabbatar da cewa jam'iyyar APC, ta samu ƙuri'u 99,830, kaso 27.61%, fiye da adadin ƙuri'un da ta samu daga gaba ɗayan jihohin yankin Kudu maso Gabas.

2. Dalilin tattalin arziƙi

Zaman Tinubu mai ido sosai akan harkokin tattalin arziƙi, zai so samun ƴan takara daga yankin Kudu maso Kudu, wanda yafi ƙarfin tattalin arziƙi kan yankin Kudu maso Gabas, wanda ya ke fama da matsalar rashin tsaro.

Kara karanta wannan

Da Dumi-Dumi: Jam'iyyar APC Ta Sanar Da Wadanda Za Su Shugabanci Majalisa Ta 10

Ana kallon yankin Kudu maso Kudu a matsayin yanki mafi ƙarfin tattalin arziƙi a Najeriya, indai ta fannin man fetur ne.

Saɓanin yankin Kudu maso Gabas, albarkatun da ke a yankin su Akpabio, da su Najeriya ke amfani wajen tafiyar da tattalin arziƙin ta. A dalilin hakan, akwai buƙatar yankin ya samu kujera mai tsoka a gwamnati.

Jigon Jam'iyyar APC Ya Bayyana Abu 1 Da Ka Iya Kawo Cikas Ga Rantsar Da Tinubu

A wani rahoton na daban kuma, kun ji yadda wani jigo a APC ya bayyana cewa babu wani ɗan kanzagi da ya isa hana a rantsar da Bola Tinubu.

Patrick Dakwom ya bayyana cewa kotu ce kawai ta ke da hurumin hana a rantsar da Tinubu.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng