Yanzu-Yanzu: Mataimakin Shugaban Jam'iyyar PDP Ya Riga Mu Gidan Gaskiya
- Mataimakin shugaban jam'iyyar PDP na ƙasa yankin Kudu maso Yamma, ya riga mu gidan gaskiya
- Hon. Olasoji Adagunodo ya kwanta dama ne a ƙasar Amurka, bayan ya yi wata ƴar gajeruwar rashin lafiya
- Majiyoyi masu ƙarfi sun tabbatar da cewa mai yankan ƙauna ta yi halin ta aƙan mamacin wanda ya ke babban jigo ne a jam'iyyar PDP
Jihar Osun - Mataimakin shugaban jam'iyyar Peoples Democratic Party (PDP), na yankin Kudu maso Yamma, Hon. Olasoji Adagunodo, ya yi bankwana da duniya.
A cewar rahoton Sahara Reporters, Adegunodo, tsohon shugaban jam'iyyar PDP ne a jihar Osun.
Hon. Seyi Adeniyi, hadimin gwamnan jihar Ogun, Ademola Adeleke, kan harkokin watsa labarai, ya tabbatar da mutuwar Olasoji, a wani rubutu da ya yi a shafin sa na Facebook, ranar Talata, 9 ga watan Mayu 2023.
A kalamansa:
DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka
“Shugaban jam'iyyar PDP na yankin Kudu maso Yamma, Soji Adagunodo ya mutu.”
An samo cewa jigon na jam'iyyar PDP ya mutu ne a ƙasar Amurka, a cewar rahoton Osun Defender, wata jarida a jihar. An dai sanar da mutuwar sa ne a ranar Talata, 9 ga watan Mayun 2023.
Shugaban matasan jam'iyyar PDP na yankin Kudu maso Yamma, Seyi Bamidele, ya tabbatar da aukuwar lamarin, inda ya ce jigon jam'iyyar, ya riga mu gidan gaskiya ne a ƙasar Amurka, rahoton jaridar Vanguard ya tabbatar.
A cewar shugaban matasan, Adagunodo, ya kwanta dama ne bayan ya yi wata ƴar gajeruwar rashin lafiya a ƙasar Amurka.
A kalamansa:
"Eh da gaske ne mataimakin shugaban jam'iyyar PDP na ƙasa, yankin Kudu maso Yamma, Hon. Soji Adagunodo, ya riga mu gidan gaskiya. Ya kwanta dama ne bayan ƴar gajeruwar rashin lafiya a ƙasar Amurka. Da yammacin nan aka sanar mana da labarin bankwanan sa da duniya."
Matar Tsohon Shugaban Majalisar Dattawa Ken Nnamani, Ta Koma Ga Mahaliccinta
A wani rahoton na daban kuma, kun ji cewa matar tsohon shugaban majalisar dattawa, Sen Ken Nnamani, ta riga mu gidan gaskiya.
Mrs Jane Nnamani, ta mutu ne a wani asibiti a cikin birnin Enugu, inda ta je a yi mata wata ƴar gajeruwar tiyata.
Asali: Legit.ng