Kotun Koli Ta Tabbatar ɗa Nasarar Gwamna Adeleke a Zaben Jihar Osun
- Kotun Ƙoli a Najeriya ta tabbatar da nasarar jam'iyyar PDP a zaben gwamnan jihar Osun da ya gabata a shekarar 2022
- Tsohon gwamna Oyetola ya ɗaukaka kara zuwa Kotun koli, inda ya kalubalanci nasarar gwamna Ademola Adeleke
- Alkalin da ya jagoranci shari'ar yace Oyetola ya gaza gamsar da Kotu zargin da ya yi na aringizon kuri'a ranar zaɓen
Kotun ƙoli a ranar Talata 9 ga watan Mayu, 2023 ta tabbatar da nasarar gwamna Ademola Adeleke na jam'iyyar PDP a zaben gwamnan jihar Osun.
Channels tv ta tattaro cewa Kotun ta jingine karar da tsohon gwamna Adegboyega Oyetola, ya ɗaukaka yana kalubalantar nasarar gwamna Adeleke.
A Hukuncin Kotun koli wanda mai shari'a Emmanuel Agim, ya karanta, ya tabbatar da hukuncin da Kotun ɗaukaka kara ta yanke game da zaben gwamnan Osun.
Legit.ng Hausa ta gano cewa Kotun ɗaukaka kara ta yanke hukuncin da ya tabbatar da nasarar Adeleke a zaben ranar 16 ga watan Yuli, 2022.
Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!
Meyasa Kotun koli ta tabbatar da nasarar Adeleke?
A rahoton Arise TV, Kotun Koli ta yanke wannan hukunci ne saboda Oyetola da jam'iyyar APC sun gaza baje kwararan hujjojin da zasu gamsar da Kotu an yi aringizon kuri'u.
Ta ce kundin dokokin zaɓe bai soke rijistar masu kaɗa kuri'a ba kuma matuƙar an yi aringizon kuri'u, za'a ga hakan ɓaro-baro a kundin rijistar masu jefa kuri'a da na'urar BVAS.
Bisa haka Kotun Allah ya isa ta bayyana cewa ana buƙatar na'urorin BVAS na runfunan zabe 744 kafin tabbatar da zargin da masu kara ke yi na aringizon kuri'a.
Yadda sakamakon zaben Osun ya nuna
Bayan kammala tattara sakamako, hukumar zabe INEC ta ayyana Adeleke na jam'iyyar PDP a matsayin wanda ya lashe zaben gwamnan Osun da kuri'u 403,371.
Wanna nasara ta ba shi damar tunbuke gwamna mai ci na jam'iyyar APC, Adegboyega Oyetola, wanda ya samu kuri'u 375,027.
Bola Tinubu Ya Roki Kotu Ta Shure Karar Jam'iyyar APM
A wani labarin kuma Zababben shugaban ƙasa ya bukaci Kotun zabe ta kori ƙarar da jam'iyyar APM ta shigar tana kalubalantar nasarar APC a zaɓen 2023
Lauyan Tinubu ya bayyana haka ne a zaman saurararon ƙarar ranar Talata, 9 ga watan Mayu, 2023.
Asali: Legit.ng