Majalisa Ta 10: Ba Zan Zama Dan Amshin Shatan Bola Tinuba Ba, Abbas Tajuddeen

Majalisa Ta 10: Ba Zan Zama Dan Amshin Shatan Bola Tinuba Ba, Abbas Tajuddeen

  • Honarabul Abbas Tajudden ya tabbatar da cewa ba zai zamo dan amshin shatan 'yan siyasa ba in ya zamu shugaban majalisar
  • Abbas dai shine wanda jam'iyyar APC ta zaba a matsayin wanda zai gaji Honarabul Gbajabiamila a majalisa ta 10
  • Dan majalisar ya bayyana irin cancantarsa na shugabancin majalisar yayin da yake kokawa kan yadda wasu ke cewa yana da rauni

Abuja - Mai neman takarar shugaban majalisar wakilai ta tarayya, Honarabul Abbas Tajudden ya ce ba zai zama dan amshin shata ba in har ya samu shugabancin majalisar.

Honarabul Abbas wanda ke wakiltar mazabar Zaria, ana sa ran shine wanda zai gaji shugabancin majalisar Femi Gbajabiamila kuma shine zabin zababben shugaban kasa, Bola Tinubu da ita kanta jam’iyyar APC.

Abbas
Honarabul Abbas Tajudden, Hoto: Leadership
Asali: Facebook

A hirarsa da gidan talabijin na Channels wanda jaridar Punch ta tattaro, Abbas ya bayyana cewa yana da abin da ake bukata na zama shugaban majalisa.

Kara karanta wannan

Abin da ya sa Arewa maso Yamma ta samu Shugabancin majalisar wakilai da dattawa a APC

A cewarsa:

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

“Me yasa suke cewa ina da rauni? Don ba ka fitowa ka ci mutuncin mutane? Don ka zama mai ba da gudumawa ga wadanda kuke aiki tare, kana mu’amala da kowa a majalisa? Don ba ka da makiya sai dai abokai?"
“Saboda ka ba da gudumawa fiye da kowa a majalisa ta 9? Kuma ka cancanta ta ko ina, shine za a ce ina da rauni?”
“Abin da nake so mutane su gane shine su je su duba cancantar kowa a cikinmu, maganan zama dan amshin shata babu shi anan, in baku manta ba a 2019 ba shugaba Buhari ne da kansa ya tura sunan Femi da Lawan a matsayin shugabannin majalisa?"
“Zamu ce kenan duk tsawon shekaru 4 da suka yi ‘yan amshin shata ne na majalisar zartaswa? ba zamu ce haka ba."

Kara karanta wannan

Baraka a Majalisa: ‘Yan Takaran Jam’iyyar APC Za Su Yi Fito na Fito da Bola Tinubu

A rahoton da muka samu, Abbas ya kara da cewa, cancantarsa ce ta sa ya bambanta da sauran ‘yan majalisar wanda hakan yasa zababben shugaban kasa ma ya ji dadin zabanshi da aka yi.

Dan majalisar ya kawo ci gaba sosai a majalisar da kuma yankinsa inda ya kawo kudururruka da suka kai 78 a majalisa ta 9.

Betara Ya Yi Watsi da Umarnin APC, Ya Nuna Sha'awarsa ta Tsayawa Takara

Honarabul Mukhtar Aliyu Betara, dan majalisar wakilai ta tarayya, ya nuna sha’awarsa ta tsayawa takarar majalisar wakilai ta 10, wanda ake sa ran za a kaddamar a watan Yuni mai zuwa.

Dan majalisar wanda shine shugaban kwamitin kasafin kudi na majalisar ya yi wannan bayani ne a ranar Litinin 8 ga watan Mayu a Abuja.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 3 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.