Kai Tsaye: Yadda Kotun Zabe Ke Zaman Sauraron Karar Atiku da PDP
Barka da zuwa shafin Legit.ng Hausa, inda zamu kawo muku abubuwan dake gudana kai tsaye daga Kotun sauraron ƙorafe-korafen zaben shugaban ƙasa a Najeriya.
Ranar Litinin 8 ga watan Mayu, Kotun ta fara zaman sauraron kararrakin zabe kuma ana ganin wannan ne zai kawo karshe kace-nace da rashin gamsuwa da zaben 25 ga watan Fabrairu.
Peter Obi ya goyi bayan Atiku
Jam'iyyar Labour Party da ɗan takarar shugaban ƙasa, Peter Obi, sun nemi Kotun zaɓe ta amince da buƙatar haska zaman sauraron karar zaben shugaban kasa a kafafen watsa labarai.
Wannan bukata ta zo daidai da wacce ɗan takarar shugaban kasa a inuwar PDP, Atiku Abubakar, ya gabatar a Kotun tun ranar zaman farko, kamar yadda Channels ta rahoto.
Kafin ɗage zaman, lauyan Peter Obi, Livy Uzoukwu, ya roki Kotu ta basu lokaci domin har yanzun ba su gama shirye-shirye kan karar da suka shigar ba.
Kotu ta ɗake karar Peter Obi zuwa mako na gaba
Kotun sauraron korafin zaben shugaban kasa a Najeriya ta ɗage ƙarar Peter Obi, ɗan takarar shugaban ƙasa a inuwar Labour Party zuwa ranar Laraba 17 ga watan Mayu, 2023.
Punch ta rahoto cewa Kotun ta ɗage zaman karar da Obi ya shigar, yana kalubalantar nasarar zababben shugaban kasa, Asiwaju Bola Ahmed Tinubu, a zaben 2023.
Mai shari'a Tsammani ya ɗauki matakin ɗage zaman zuwa Laraba mai zuwa bisa la'akari da bukatar kowane ɓangare.
Tinubu ya maida martani kan janyewar APP
Lauyan zababben shugaban ƙasa, Wole Olanipekun, ya ce Tinubu ba zai yi jayayya da buƙatar jam'iyyar APP na janye ƙara ba, inda ya ƙara da cewa ba ya neman ko sisin kwabo daga hannu APP.
Bayan haka ne shugaban kwamitin alkalan Kotun, mai shari'a Haruna Tsammani ya kori ƙarar ba tare da tarar ko sisi ba.
Daga nan kuma Kotun ta sanar da tafiya hutu kuma za'a dawo da misalin ƙarfe 2:00 na rana domin ci gaba da sauraron karar Peter Obi, kamar yadda Dailytrust ta rahoto.
APP Ta Janye Karar kalubalantar nasarar Tinubu
Jam'iyyar Action Peoples Party (APP) ta buƙaci janye ƙarar da ta shigar gaban Kotu, tana kalubalantar nasarar Bola Tinubu, kamar yadda The Cable ta rahoto.
Haka nan lauyan APP, Obed Agu, ya roki Kotun sauraron korafin zaben shugaban kasa ta shure ƙarat kana ta yi fatali da ita baki ɗaya.
Zaman Kotun zabe ya shiga rana ta 3
Barka da zuwa shafin Legit.ng Hausa inda zamu kawo muku abinda ke faruwa a rana ta 3 kai tsaye daga Kotun sauraron karar zaben shugaban kasa mai zama a Abuja.
A yau Laraba, 10 ga watan Mayu, Kotu zata kasa kunne ta saurari buƙatun ɗan takarar shugaban ƙasa a inuwar LP, Peter Obi, kan sakamakon zaben shugaban ƙasa.
Idan baku manta ba, shugaban kwamitin Alƙalai, mai shari'a Haruna Tsammani, ranar Litinin, ya ɗage zaman zuwa Laraba domin sauraron kowane ɓangare a karar Obi da LP.
Da misalin karfe 2:00 na rana za'a ci gaba zaman kuma Kotu zata duba yadda ɓangarori suka yi biyayya ga umarninta na fito muhimman batutuwan da za'a tattauna yayin ainihin zaman shari'ar.
A cewar Daily Trust, Obi da LP zasu gabatar da buƙatar Kotu ta sahale a nuna yadda zaman sauraron ƙararrakin ke gudana kai tsaye a kafafen watsa labarai.
Kotu ta ɗage sauraron karar Atiku
Alkalin Kotun zaɓe, mai shari'a Haruna Tsammani, ya sanar da ɗage zaman sauraron ƙarar Atiku Abubakar zuwa ranar 11 ga watan Mayu, 2023.
Tsammani ya kara da cewa sabbin ɓukatun da lauyoyin Tinubu suka gabatar wanda suka nemi a kori karar Atiku tun yanzu, duk Kotu zata saurare su ranar Asabar.
Legit.ng Hausa ta tattaro cewa Kotun zaɓen zata yanke hukunci kan buƙatar Atiku na watsa yadda zaman Kotun ke gudana kai tsaye a kafafen watsa labarai, ranar Alhamis.
Tinubu ya buƙaci Kotu ta yi fatali da ƙarar Atiku
Lauyan zababben shugaban ƙasa, Bola Ahmed Tinubu, ya nemi Kotun sauraron ƙarar zaben shugaban ƙasa ta yi watsi da ƙarar Atiku Abubakar.
Akin Olujimi (SAN) ya bayyana haka ne yayin martani kan ko tawagar lauyoyin Tinubu sun cike amsoshin da ke kunshe a Fam TF 008 na ƙorafin Atiku.
Lauyan ya ce, "Eh," amma sun gabatar da sabbin buƙatu wanda suka roki Kotu ta shure ƙorafe-ƙorafen baki ɗaya, rahoton Daily Trust.
An karya alƙawurra da yawa a zaben 2023 - Atiku
Lauyan Atiku Abubakar, Chris Uche (SAN) ya shaida wa Kotun sauraron karar zaben shugaban ƙasa cewa, "An karya duk wata yarjejeniya a babban zaɓen 2023."
Babban Lauyan ya faɗi hake yayin da yake nuna goyon bayan cewa ba dole bane sai an bi wasu matakain da Kotu ta zaɓa yayin zaman sauraron ƙarar zaben shugaban kasa.
Mista Uche ya ce sa'ilin da mai shari'a Tsammani ya faɗa masa sun riga sun amince da matakan tuntuni, shugaban kwamitin Alkalai ya maida masa maratani da, "Wannan kai ya shafa."
An fara sauraron karar Atiku
Kotun sauraron karar zaben shugaban ƙasa ta fara sauraron ƙarar da ɗan takarar shugaban kasa a inuwar PDP, Atiku Abubakar, ya shigar yana kalubalantar nasarar Tinubu.
Atiku na ganin hukumar zabe mai zaman kanta (INEC) ta karya wasu dokokin zaɓe kuma ta saɓawa alkawurran da ta ɗauka game da babban zaɓen 2023.
Kotu ta ɗage sauraron karar APM
Shugaban kwamitin alkalai 5, Mai shari'a Haruna Tsammani, ya ɗage sauraron ƙorafin jam'iyyar Allied Peoples Movement (APM) zuwa ranar Alhamis, 11 ga watan Mayu, 2023.
Alkalin ya ce hakan zai baiwa kowane ɓangare damar duba bukatu da kuma batutuwan da zasu tsoma baki a zaman shari'a da wanda basu shafe su ba.
Jam'iyyar APM ta nemi Kotu ta soke takarar Bola Tinubu saboda sauya sunan abokin takararsa daga Ibrahin Masari zuwa Sanata Kashim Shettima, Channels ta rahoto.
Kotu zata fara sauraron korafin Atiku da APM
Kotun sauraron ƙorafin zaben shugaban ƙasa ta shirya fara zama na biyu, wanda zata saurari ƙarar Atiku Abubakar na jam'iyyar PDP da ƙarar jam'iyyar APM, kamar yadda rahoto ya tabbatar.