Majalisa Ta 10: APC Ba Ta Son Ta Ba Wa Inyamurai Jagoranci, Sanata Shehu Sani

Majalisa Ta 10: APC Ba Ta Son Ta Ba Wa Inyamurai Jagoranci, Sanata Shehu Sani

  • Sanata Shehu Sani ya bayyana cewa jam'iyya mai mulki tana nuna rashin yarda da wasu daga Kudu masu Gabas wajen shugabancin majalisar dattawa ta 10
  • Sanatan ya bayyana haka ne a shafinsa na Twitter a ranar Lahadi 7 ga watan Mayu na wannan shekara in da ya gargadi jam’iyyar APC
  • Ya ce da wadanda suka shiga jam'iyyar APC ta bayan fage da ta kofa dukkansu ba a yarda dasu ba ba waje shugabancin majalisar

Kaduna - Tsohon Sanata a Najeriya kuma jigo a jam’iyyar PDP A Kaduna, Shehu Sani ya ce alamu sun bayyana cewa jam’iyya mai mulki ta APC ba ta yarda da ‘yan siyasa daga Kudu maso Gabas ba wurin ba su shugabancin majalisar dattawa ta 10.

Tsohon sanatan, wanda ya wakilci Kaduna ta tsakiya a jam’iyyar PDP a majalisa ta 8, ya bayyana hakan ne ta shafinsa na Twitter a ranar Lahadi, 7 ga watan Mayu.

Kara karanta wannan

Za Mu Yi Amfani da Rudanin APC, Mu Tsaida Shugabannin Majalisa Inji Sauran Jam’iyyu

Jaridar Tribune ta tattaro sanatan yana cewa Inyamurai 'yan siyasa bai kamata su kwallafa ransu akan shugabancin majalisar ba, ganin yadda suka shigo jam'iyyar.

Shehu Sani
Sanata Shehu Sani, Hoto: Daily Post
Source: Facebook

Sanata Shehu ya ce:

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

“Ya fara bayyana cewa wadanda suka shiga jam’iyyar APC daga Kudu maso Gabas ta taga da wadanda suka shiga ta kofa duk ba a yarda dasu a shugabanci."

Me ya jawo maganar

Wannan bayani na sanatan yana da nasaba da shugabancin majalisar dattawa ta 10 da ‘yan siyasa a ko ina a kasar ke kokarin ganin sun samu daga jam'iyya mai mulki ta APC za ta kaddamar a watan Yuni na wannan shekara.

Jaridar Legit Hausa ta ruwaito Gwamnan Kano, Abdullahi Ganduje yana cewa sun riga sun yanke hukunci cewa tsohon gwamnan Akwa Ibom ne zai zama shugaban majalisar dattawa ta 10.

Majalisa ta 10: Ganduje Ya Fadi Wanda Zai Zama Shugaban Majalisar Dattawar Najeriya

A wani labarin, Gwamna Abdullahi Umar Ganduje na jihar Kano ya bada karin haske game da wanda zai zama shugaban majalisar dattawar Najeriya ta 10.

Kara karanta wannan

Buhari: Abin da Ya Sa Na Ki Fitowa Karara In Goyi Bayan Magajina a Zaben Gwanin APC

Gwamnan yayi wannan bayani ne a wani taro a Calabar, baban birnin jihar Kuros Riba, ya ce tsohon ministan Neja Delta, Godswill Akpabio shi ne zai zama shugaban majalisar dattawa.

Gwamnan ya ce tsohon ministan ya taka muhimmiyar rawa wurin kawo ci gaba a kasar nan, don haka shi kadai ya dace da wannan shugabanci.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 5 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.