Jerin Manyan Alkalai 5 da Zasu Jagorancin Shari'a Kan Zaben Shugaban Kasa
Rana ba ta karya, ranar da yan Najeriya ke ta dakon zuwanta ta zo, a yau Litinin 8 ga watan Mayu, 2023, Kotun sauraron ƙorafe-korafen da suka shafi zaɓen shugaban ƙasa zata fara zama.
Kamar yadda ta tsara Kotun zata saurari kararrakin da aka shigar gabanta wanda suka kalubalanci sakamakon babban zaben shugaban kasan da ya gabata ranar 25 ga watan Fabrairu, 2023.
Wannan shari'a ka iya kawo karshen muharawa da cece-kucen da ake kan sakamakon zaben da hukumar zabe mai zaman kanta (INEC) ta sanar.
Shugaban kwamitin alƙalai 5 da zasu jagoranci zaman shari'ar, mai shari'a Haruna Tsammani, ya buɗe zaman Kotu da jawabinsa da misalin ƙarfe 9:15 na safiyar Litinin.
Legit.ng Hausa ta tataro muku cikakken jerin sunayen Alkalan guda 5, ga su kamar haka;
Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!
1. Mai shari'a Haruna Tsammani (Shugaba)
2. Mai shari'a Stephen Adah
3. Mai shari'a Monsuraf Bolaji Yusuf
4. Mai shari'a Boloukuoromo Moses Ugo
5. Mai shari'a Abbah Muhammed.
Idan baku manta ba INEC ta ayyana ɗan takarar APC, Asiwaju Bola Ahmed Tinubu, a matsayin wanda ya lashe zaben shugaban kasan 2023 da ƙuri'u mafi rinjaye.
Sai dai jam'iyyun adawa da yan takararsu sun ce sam ba su yarda ba, INEC ta tafka kura-kurai yayin zaben ranar 25 ga watan Fabrairu, 2023.
Wasu jam'iyyun sun yi musun cewa Tinubu da abokin takararsa, Kashim Shettima ba su cancanci shiga zaɓen ba, don haka suka garzaya Kotu da nufin ta bi musu haƙƙinsu.
A yau ne Kotun sauraron ƙararrakin zabe zata fara zama kuma kamar yadda muka faɗa muku, zamu kawo muku duk abinda ke gudana kai tsaye a nan.
Kotun Koli Ta Sanya Ranar Yanke Hukunci Kan Zaben Gwamnan Osun
A wani labarin na daban kuma Kotun koli zata yanke hukunci kan karar zaben gwamna jihar Osun
Tsohon gwamnan jihar, Oyetola, ya kalubalanci nasarar da gwamna Ademola Adeleke na jam'iyyar PDP ya samu a zaben ranar 16 ga watan Yuli, 2022.
A zaman yau Talata, Kotun koli ta ce ranar Talata 9 ga watan Mayu, zata yanke hukunci kan me gaskiya tsakanin Oyetola da Adeleke.
Asali: Legit.ng