Gaskiya Ta Bayyana Kan Dalilin Gwamnonin Arewa Na Goyon Bayan Bola Tinubu
- Gwamnan jihar Plateau, Simon Lalong, ya bayyana dalilin gwamnonin Arewancin Najeriya na goyon bayan komawar mulki Kudu
- Lalong ya ce ba wai goyon bayan Tinubu ba ne ya sanya suka ƙeƙashe ƙasa cewa sai mulki ya koma Kudu
- A cewar sa sun ɗauki matakin ne domin tabbatar da gaskiya da adalci a ƙasar nan domin wanzuwar zaman lafiya da haɗin kai
Jihar Nasarawa - Shugaban ƙungiyar gwamnonin Arewacin Najeriya kuma gwamnan jihar Plateau, Simon Lalong, ya bayyana cewa ba Bola Tinubu ba ne a ran su lokacin da suka goyi bayan komawar mulki zuwa yankin Kudancin ƙasar nan.
Lalong, wanda ya yi babban darektan ƙungiyar yaƙin neman zaɓen shugaban ƙasa na Bola Tinubu, ya ce sun goyi bayan shugaban ƙasa ya fito daga Kudu ne saboda zaman lafiya, kwanciyar da daidaito a Najeriya, domin yin koyi da riƙon gaskiya, adalci irin na Sir Ahmadu Bello.
Tribune tace Lalong ya yi magana ne wajen lakcar shekara-shekara ta tunawa da Sir Ahmadu Bello ta 9, kan shugabanci da jagoranci mai kyau, wacce aka gudanar a Lafia babban birnin jihar Nasarawa.
A wata sanarwa da kakakin gwamnan Macham Makut, ya fitar, ya bayyana cewa:
DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka
"Lokacin da na jagoranci takwarorina gwamnonin Arewa domin ganin mulki ya koma Kudu, ba wai don muna son Asiwaju ya zama shugaban ƙasa ba ne, sai kawai domin muna son tabbatar da gaskiya da adalci sun samu a ƙasar mu domin haɗin kai, kwanciyar hankali da lumana."
"Wannan shine abinda mu ka yi amanna cewa uban mu Allah ya yi masa rahama, Sir Ahmadu Bello, zai yi a cikin irin wannan halin."
"Cikin sa'a kuma sai deliget ɗin jam'iyya suka zaɓi Asiwaju, wanda daga ƙarshe ƴan Najeriya suka aminta da shi inda suka zaɓe shi a matsayin shugaban ƙasa."
Lalong ya kuma roƙi ƴan Najeriya da su marawa zaɓaɓɓen shugaban ƙasar baya, yayin da ya ke ƙoƙarin ɗarewa kan karagar mulkin ƙasar nan, cewar rahoton Ripples Nigeria.
Tinubu ya Ayyana Wadanda Yake So, Yari Ya Ce Zababben Shugaban Yayi Kadan
A wani rahoton na daban kuma, rigima na nan kwance a jam'iyyar APC kan shugabancin majalisar dattawa.
Tsohon gwamnan jihar Zamfara, Abdul'aziz Yari, ya yi fatali da zaɓin Bola Tinubu na wanda zai shugabanci majalisar dattawa.
Asali: Legit.ng