Rantsar Da Tinubu: Yadda Kotun Zabe Za Ta Iya Karɓe Nasarar Zababben Shugaban Kasa, Fitaccen Lauya Ya Magantu
- Lauya Festus Ogun, masanin dokokin zaɓe da na 'yancin ɗan adam ya ce za a iya karɓe kujera Tinubu ko da bayan rantsar da shi ne a ranar 29, muddun masu ƙarar za su iya kare hujjojin su
- Ogun ya ja hankalin masu cewa ba za a rantsar da Tinubu a ranar 29 ba kan cewa doka ba ta bada damar hakan ba
- Lauyan ya ce duk wanda INEC ta sanar ya ci zaɓe babu mai iya dakatar da rantsar da shi sai kotu, kuma kotun ƙarar zaɓe ba ta hana a rantsar da mutum
Ikeja, Lagos - Sanannan lauya masanin dokar ƙasa ya bayyana cewa za a iya rantsar da zaɓaɓɓen shugaban ƙasa Bola Tinubu ranar 29 daga baya kuma a zo a karɓe kujerar ta shi muddun dai masu ƙarar za su iya kare hujjojinsu a gaban kotu.
Legit.ng ta wallafa cewa lauyan wato Festus Ogun ya janyo hankalin masu bugun ƙirjin cewa ba za a rantsar da Tinubu a ranar 29 ga watan Mayu ba, wanda ya bayyana hakan a matsayin wata magana mai haɗari. Ya ce duk wasu kiraye-kirayen da ke nuni da a dakatar da rantsuwar ta Tinubu ta saɓa ma doka.
Ba za a iya dakatar da rantsar da Tinubu ba
Festus ya rubuta a shafinsa na Tuwita:
DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar
“Kotun sauraron ƙararrakin zaɓe za ta iya karɓe kujerar mutumin da har aka bada sanarwar ya ci zaɓe sannan kuma har aka rantsar da shi indai su masu ƙarar za su iya bayar da gamsassun hujjoji.”
“Maganar da wasu suke yi kan batun cewa rantsuwa da za a yi a ranar 29 ga wata ba za ta yi wu ba abu ne mai haɗari kuma wanda ya saɓa ma doka.”
Da ya ke ƙara jawabi kan abinda doka ta tanada, Ogun ya ce duk mutumin da INEC ta riga da ta sanar ya ci to dole ne a rantsar da shi, sai dai in kotu ce ta dakatar da rantsuwar, wanda kuma kotun sauraron ƙararrakin zaɓe ba za ta yi hakan ba.
Kotun sauraron ƙarar zaɓen dai za ta fara sauraron koke-koken da aka shigar dangane da zaɓen na shugaban ƙasa a ranar 8 ga wannan wata da muke ciki.
Atiku da Peter Obi sun yi watsi da sakamakon zaɓen
'Yan takarar ɓangaren adawa a zaɓen shugaban ƙasar musamman ma dai Atiku Abubakar na jam'iyyar PDP da kuma Peter Obi na Labour Party sun ƙi amincewa da sakamakon zaɓen domin ko a cewar su an tafka almundahana a ciki. Hakan ne ya sanya suka shigar da ƙara a kotun sauraron ƙararrakin zaɓen.
Ana cikin hakan ne kuma aka ji wani aminin Atiku, Timi Frank wanda kuma shine tsohon sakataren watsa labarai na jam'iyyar APC ya ɓara yana faɗin cewa kaso tamanin cikin ɗari na mutanen da za su amfana da gwamnatin Tinubu duk tsofaffin 'yan siyasar da su ka yi ƙaurin suna ne kan cin hanci da rashawa.
Kotu ta yanke wa wasu mutane hukuncin shekaru 5 saboda da satar naman kaji
A wani labarin na daban kuma, kunji yadda wata kotu ta yanke wa wasu mutane 2 hukuncin zaman shekaru 5 a gidan yari bisa laifin satar fuka-fukan kaji a gidan abincin da suke aiki.
Wannan lamari dai ya faru ne a Kumasi babban birnin ƙasar Ghana inda mutanen guda 2 da ke aiki a wani gidan abinci mai suna Pizzaman aka tuhume su da yin sama da faɗi da naman kaji da kuma man girki da ake amfani da shi a gidan.
Asali: Legit.ng