“Dangantakar Wike Da APC Ba Za Ta Kai Ko’ina Ba”: Primate Ayodele Ya Yi Hasashe
- Primate Elijah Ayodele ya yi hasashen cewa dangantakar da ke tsakanin Gwamna Nyesom Wike da jam'iyyar APC ba za ta yi karko ba
- Malamin ya ce nad-naden mukamai zai raba kan APC, sannan na kewaye da jam'iyyar mai mulki za su yaki gwamnanan na Ribas
- A cewar malamin addinin, za a ci amanar Wike sosai saboda shima ya ci amanar jam'iyyarsa
Primate Elijah Ayodele shugaban cocin INRI Evangelical Spiritual Church ya bayyana cewa dangantakar da ke tsakanin Gwamna Nyesom Wike na jihar Ribas da jam'iyyar All Progressives Congress (APC) ba zai yi karko ba.
Malamin ya bayyana haka ne a cikin wata sanarwa dauke da sa hannun hadiminsa, Osho Oluwatosin a ranar Juma'a, 5 ga watan Mayu, jaridar Tribune ta rahoto.
A cewar malamin addinin, gwamnatin Bola Tinubu za ta yaki gwamnan na jihar Ribas mai barin gado.
Abun da Primate Ayodele ya yi hasashe game da Gwamna Wike, Bola Tinubu da APC
Ayodele ya ce bayan bikin rantsar da zababben shugaban kasa Bola Tinubu, a ranar 29 ga watan Mayu, abubuwa da dama za su sauya kuma wadanda ke tsammanin samun manyan mukamai na iya tashi a tutar babu saboda abun da zai tarwasa APC mai mulki shine nade-naden mukamai.
Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!
Wani bangare na jawabinsa ya ce:
"Dangantakar Wike da APC ba zai kai ko'ina ba. 'Cabals' za su yake shi ba da wasa ba, kuma zai biya bashi ba da wasa ba, amma ba zai fahimci haka ba yanzu. APC za ta koya masa babban darasi, ciki harda sauran wadanda suka sauya sheka a PDP."
Malamin ya kuma bukaci yan Najeriya da su guji yaki saboda kowani dan siyasa, yana mai cewar babu wanda ya cancanci haka a cikinsu.
A cewarsa shugabannin addini, yan siyasar Najeriya na iya sadaukar da magoya bayansu ne kawai don cin ribar kansu.
Ya jaddada cewar APC za ta ci amanar Gwamna Wike sosai saboda shima ya ci amanar jam'iyyarsa.
Yaki da cin hanci da rashawa: Tinubu ya yaba ma gwamna Wike
A wani labarin, mun ji cewa Bola Tinubu, zababben shugaban kasa ya ce gwamnan jihar Ribas, Nyesom Wike ya cancanci ayi koyi da shi a bangaren yaki da cin hanci da rashawa.
Asali: Legit.ng