Gwamna Ganduje Ya Fadi Sanatan da Zai Gaji Lawan, Ya Zama Sabon Shugaban Majalisa
- Abdullahi Umar Ganduje ya nuna tamkar Godswill Akpabio har ya zama shugaban majalisar dattawa ne
- Gwamnan jihar Kano ya ce Gwamnonin jihohin APC sun tsaida matsaya a kan wanda zai rike Majalisa
- Ben Ayade ya ji dadi da ‘yan kungiyar PGF su ka gamsu da Sanata Akpabio daga yankin Kudu maso kudu
Cross River - Gwamna Abdullahi Umar Ganduje na jihar Kano ya ce tsohon Gwamnan Akwa Ibom, Godswill Akpabio zai zama shugaban majalisa.
Dr. Abdullahi Umar Ganduje ya fadawa Duniya cewa a game da batun majalisa, aikin gama ya gama, jaridar Tribune ta fitar da rahoton nan a ranar Juma’a.
Mai girma Gwamnan bai iya tabbatar da wannan ne matakin da jam’iyyarsa ta APC ta dauka ba.
Bayanin Gwamnan na jihar Kano ya fio ne a lokacin da ya yi wani zama da takwaransa na Kuros Ribas, Mai girma Gwamna Ben Ayade a garin Kalaba.
Jawabin Abdullahi Umar Ganduje
Shugaban majalisar dattawa zai fito daga yankin Kudu maso kudu, kuma ba kowa ne wannan ba sai tsohon Gwamnan jihar Akwa Ibom.
DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka
Gwamnan da ya fita dabam, Minista da ya fita dabam wanda zai zama shugaban majalisa da ya fita dabam, mun dauki wannan matsayar.
Ina mai tabbatar maku mu na jiran ranar wanka ne, lokacin da zai zama shugaban majalisa.
-Abdullahi Umar Ganduje
Matsayar Gwamnonin APC
Rahoton Premium Times ya ce Gwamna Ganduje ya yi bayani ne da yawun bakin kungiyar gwamnonin jam’iyyar APC a kasar nan watau PGF.
Kafin yanzu kungiyar sun yanke shawara cewa shugaban majalisa ya zama ya fito daga jihohin Kudu maso kudu ko kuwa Kudu maso gabashin kasar.
A wani bidiyo da yake yawo a shafin gidan talabijin AIT, an ji Gwamnan Kano yana cewa sauran Gwamnonin APC sun gamsu su goyi bayan Akpabio.
Dr. Ganduje ya ce babu wanda zai canza tsarin da suka fitowa jam’iyyar APC mai mulki da shi
Ayade ya ji dadi
Jaridar ta ce Gwamna Ben Ayade ya ji dadin matsayar da abokan aikinsa su ka dauka, su ka yarda a samu shugaban majalisa daga yankin da ya fito.
Gwamnan ya godewa takwarorinsa a APC, ya ce su na farin ciki da wannan dama ta samun shugaban majalisa daga jihar da ke makwabtaka da su.
Asali: Legit.ng