Daga Karshe An Bayyana Ainihin Dalilin Da Ya Sanya Osinbajo Ya Yi Takara Da Tinubu

Daga Karshe An Bayyana Ainihin Dalilin Da Ya Sanya Osinbajo Ya Yi Takara Da Tinubu

  • Na kusa da mataimakin shugaban ƙasa, Farfesa Yemi Osinbajo, ya bayyana ainihin dalilin da ya sanya ya nemi takarar shuagaban ƙasa
  • Laolu Akande ya ce son cigaban al'umma ne ya sanya Osinbajo neman ɗarewa kan kujerar shugabancin ƙasar nan
  • Takarar da Osinbajo ya yi ta shugaban ƙasar, ta sanya wasu na ganin dangantaka ta yi tsami tsakanin sa da Tinubu

Abuja - Laolu Akande, kakakin mataimakin shugaban ƙasa, Yemi Osinbajo, ya bayyana cewa son cigaban al'umma ne ya sanya mataimakin shugaban ƙasar, ya nemi tikitin takarar shugaban ƙasa a jam'iyyar APC, cewar rahoton The Cable.

Osinbajo yana daga cikin ƴan takarar da suka fafata a zaɓen fidda gwani na shugaban ƙasa na jam'iyyar APC, wanda Bola Tinubu ya lashe.

Cigaban al'umma ya sanya Osinbajo takara da Tinubu
Bola Tiunbu da Osinbajo a wajen wani taro Hoto: Premiumtimes.com
Asali: UGC

Takarar da ya yi da Tinubu ta sanya ya sha caccaka daga ƴaƴan jam'iyyar APC na jihar Legas, inda wasu ke cewa ya ci amanar Tinubu.

Kara karanta wannan

Akwai Matsala: Malamin Addini Ya Hango Gagarumar Matsala a Kawancen Tinubu Da Gwamnan PDP

Osinbajo ya yi aiki a ƙarƙashin Bola Tinubu, lokacin yana gwamnan jihar Legas, inda ya riƙe muƙamin Antoni Janar na jihar.

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

Da yake magana a yayin tattaunawa da gidan talbijin na Channels tv, Akande ya ce Osinbajo, ya yi takara saboda ya yi amanna cewa yana da dukkanin ƙwarewa da cancantar da ofishin shugaban ƙasa ya ke da buƙata, rahoton Vanguard ya tabbatar.

A kalamansa:

"Abinda ya ke da muhimmanci shine ɗaukar matakin da kake so domin cigaban al'umma. Cigaban al'umma shine abin kallo."
"Zama mataimakin shugaban ƙasa har na tsawon shekara 8, sannan da irin salon shugabancin da ya nuna, da ɗumbin aikin da ya yi."
"Tsantsar fahimtar yin abubuwan da yakamata a yi, sannan da ƙwarewar da ya nuna lokacin da ya ɗauki ragamar shugabanci a dalilin rashin shugaban ƙasa."

Kara karanta wannan

"Abu 1 Mu Ke Jira", Daga Karshe APC Ta Bayyana Dalilin Rashin Fitar Da Tsarin Shugabancin Majalisa Ta 10

"Ya yi abinda ya ke da buƙatar ya yi sannan jam'iyya ta yanke hukuncin ta, ya wuce wajen da sanin cewa ya yi abinda ya dace."

Osinbajo dai bai wani halarci yaƙin neman zaɓen shugaban ƙasa ba, lokacin da ake tunkarar zaɓe.

Daga ƙarshe dai Tinubu ya lallasa Atiku Abubakar na jam'iyyar Peoples Democratic Party (PDP) da Peter Obi na jam'iyyar Labour Party (LP), a zaɓen shugaban ƙasar.

Rundunar Soji Ya Magantu Kan Masu Shirin Hana Bikin Rantsar da Tinubu

A wani rahoton na daban kuma, kun ji yadda hukumar sojin Najeriya ta yi jan kune ga masu shirin tayar da ƙayar a lokacin rantsar da Bola Tinubu.

Hukumar ta yi gargaɗin cewa duk wasu masu shirya wani tuggu a bayan fage da su shiga taitayin su.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng