Jam’iyyun Adawa Sun Yi Taro, An Tsara Yadda Za a Yaki ‘Yan Takaran APC a Majalisa
- Wasu da za su je majalisar tarayya a karkashin jam’iyyun adawa su na cigaba da shirin yakar APC
- ‘Yan hamayya za su tsaida ‘dan takaransu na shugaba da mataimakin shugaban majalisar wakilai
- Idan ‘yan APC ba su hada-kai ba, sauran ‘yan adawa za su iya kawo masu matsala a zaben bana
Abuja - ‘Ya ‘yan jam’iyyar hamayya a majalisar wakilan tarayya sun kara kaimi wajen ganin an mamayi APC, sun tsaida ‘dan takarar shugaban majalisa.
Rahotanni daga Tribune sun nuna ‘yan adawar sun yi wani taro a Transcorp Hilton a ranar Talata, a karshe suka cin ma matsaya za su shiga takarar majalisa.
La’akari da yawansu, ‘yan adawan za su hada-kai a gefe guda domin su iya fito da wadanda suke so ya zama shugaban majalisar wakilai da mataimakinsa.
A yunkurin ganin sun yi wa APC mai rinjaye kafa, jam’iyyun adawar sun kafa wani kwamiti mai mutum 11 da zai zakulo wadanda suka cancanta da takara.
Kwamiti zai nemo 'Yan takara
Aikin kwamitin shi ne duba zababbun ‘yan majalisar wakilan da za su samu karbuwa.
DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka
A karshen taron da suka yi a otel din a farkon makon nan, an fitar da jawabi ‘yan adawa za su hada-kansu ganin su ke da fiye da 50% na kujerun majalisa.
Marasa rinjaye masu rinjaye
A rahoton Daily Trust, an ji jam’iyyar APC ta na da wakilai 178, amma jam’iyyun PDP, SDP, NNPP, YPP, APGA da LP a gefe guda su na da mutum 180.
Akwai kujeru biyu a Akwa Ibom da Ondo da ba a san jam’iyyar da za ta lashe su ba.
Sakataren tafiyar, Efosa Imasuen ya ce a shirye su ke su yaki APC domin sun fi jam’iyya mai mulki yawan kujeru, kuma su na tare da wasu ‘Yan APC.
A cewar Hon. Imasuen, akwai wasu da suka lashe zabe a jam’iyyar APC da suke goyon bayansu, an rahoto shi yana cewa za su yi abin da suka ga dama.
"Babu inda za a je!" - Hon. Monguno
Shugaba masu tsawatarwa a majalisa, Mohammed Tahir Monguno ya ce ‘yan adawan ba za su kai ko ina ba domin kan APC a hade yake kamar a 2019.
Masu wannan shiri sun nuna babu abin da ya dame su da inda jam’iyyar APC ta warewa kujeru, suka ce hakan bai yi aiki wajen neman shugaban kasa ba.
AbdulAziz Yari ya dage
Kwanaki uku da suka wuce AbdulAziz Yari ya sa labule da Shugaba Muhammadu Buhari, an ji labari 'dan siyasar ya dage wajen takarar shugaban majalisa.
Tsohon Gwamnan Zamfara ya huro wuta, da gaske yake takarar shugabancin majalisar dattawa, kuma ya na samun goyon bayan wasu manya a siyasa.
Asali: Legit.ng