Tsohon Gwamnan Zamfara Ya Samu Goyon Bayan Na Kusa da Shugaba Buhari a Zaben Majalisa

Tsohon Gwamnan Zamfara Ya Samu Goyon Bayan Na Kusa da Shugaba Buhari a Zaben Majalisa

  • Takarar AbdulAziz Yari ta samun karbuwa a wajen ‘yan siyasa da wadanda ake damawa da su
  • Tsohon Gwamnan na Zamfara ya ci zaben Sanata, ya fara hangen shugabancin majalisar dattawa
  • Shugaban kungiyar Tinubu/Shettima Network yana goyon bayan AbdulAziz Yari dari bisa dari

Abuja - Wani wanda ake ganin yana da kusanci da Mai girma shugaba Muhammadu Buhari, Kailani Muhammad ya na tare da AbdulAziz Yari.

Punch ta ce Alhaji AbdulAziz Yari yana cikin wadanda suke goyon bayan AbdulAziz Yari ya zama shugaban majalisar dattawa a zaben da za ayi.

Hakan yana nufin ‘yan kungiyar Tinubu/Shettima Network sun marawa tsohon Gwamnan Zamfara baya a neman hawa kujera ta uku a girma.

‘Yan Tinubu/Shettima Network su na ganin a matsayinsa na tsohon shugaban kungiyar gwamnonin Najeriya, Yari ya cancanci rike majalisa.

Kungiyar TSN ta bi

Kara karanta wannan

"Na Yi Nadamar Mulkin Buhari Saboda Manyan Abu 2 da Ya Kawo" Tsohon Makusancin Buhari Ya Tona Asiri

Haka zalika tun da ya fito daga Arewa ta yamma, ‘yan TSN su na tare da zababben Sanatan.

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

Kailani wanda tun ana jam’iyyar CPC yake goyon bayan Muhammadu Buhari, ya kira taron manema labarai a garin Kaduna, ya shaida matsayarsa.

Tsohon Gwamnan Zamfara
AbdulAziz Yari tare da Shugaban kasa Hoto: @BuhariSallauOnline
Asali: Facebook

AbdulAziz Yari bai da sa'a

Vanguard ta ce Shugaban kungiyar ya nuna duk masu neman shugabancin majalisa sun dace, amma idan ana batun cancanta, Yari ne a kan gaba.

A cewarsa, a zaben shugaban kasa da aka yi a Fubrairun bana, Yari ya ba jam’iyyar APC kuri’u 2,700,000, saboda haka ya kamata ayi la’akari da shi.

Idan aka duba abin ta fuskar adalci, ‘dan siyasar ya ce daga Arewa maso yammacin kasar nan ya kamata a lalubo wanda zai gaji Sanata Ahmad Lawan.

Kafin ya kira taron ‘yan jaridar, shugaban TSG ya ce ya yi nazarin masu harin zama shugaban majalisar dattawa, a nan ya fahimci wanda ya fi dacewa.

Kara karanta wannan

Zababbun Sanatocin APC 2 Su na Rububi a Kan Kuri’un ‘Yan PDP a Majalisar Dattawa

Jihohin Kudu maso kudu sun hadu sun ba Tinubu kuri’u 40,000 ne a zaben da ya wuce, hakan ya jawo TSG ke ganin ya kamata a sakawa Arewa.

Meya hana NNPP shiga kotu?

Idan da akwai wanda zai je kotun sauraron karar zabe, ya yi nasara a kalubalantar jam’iyyar APC, an rahoto Injiniya Buba Galadima yana cewa NNPP ce.

Da yake bada dalilansa, Galadima ya ce tun farko ba a a daura sunan NNPP a takardar kada kuri’a ba, wannan ya jawo ba a ga jam’iyyar Kwankwaso ba.

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng