Wata Sabuwa: Jigon Jam'iyyar APC Ya Yi Wa Tsohon Sarkin Kano Wankin Babban Bargo Kan Abu 1
- Kalaman da Sanusi Lamido Sanusi ya yi akan rashin samun Osinbajo a matsayin shugaban ƙasa, ba su yi wa jigon APC daɗi ba
- Joe Igbokwe ya mayar da martani mai kaushi ga tsohon sarkin, inda ya kira shi da maƙiyin APC
- Jigon ya ce da jam'iyyar APC, ta ba Osinbajo takara a zaben shugaban ƙasa da ba ta kai labari ba
Jihar Legas - Mai bai wa gwamnan jihar Legas shawara ta musamman kan magudanun ruwa, Joe Igbokwe, ya bayyana cewa jam'iyyar All Progressives Congress (APC), da ta sha a zaɓen shugaban ƙasa idan Farfesa Osinbajo ne ɗan takarar ta.
Joe Igbokwe ya bayyana cewa da ace Osinbajo ya samu tikitin takarar shugaban ƙasa a ƙarƙashin inuwar jam'iyyar, to da Atiku Abubakar, ɗan takarar jam'iyyar PDP a zaɓen shugaban ƙasar, ya yi nasara a kan sa, cewar rahoton Vanguard.
Mai Neman Shugabancin Majalisar Dattawa Ya Kebe Da Shugaba Buhari, Ya Bayyana Yankin Da Ya Cancanci Kujerar
Kalaman Igbokwe na zuwa ne bayan iƙirarin da tsohon sarkin Kano, Sanusi Lamido Sanusi, ya yi na cewa Najeriya ta yi asara a rashin samun mutum kamar Osinbajo, a matsayin shugaban ƙasa.
Sai dai, Igbokwe, a wani rubutu da ya yi a shafin sa na Facebook ranar Laraba, ya yi wa tsohon gwamnan babban bankin Najeriya (CBN), shaguɓe.
DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka
A cewar Igbokwe, da Osinbajo jam'iyyar APC, ta ba tikitin takarar shugaban ƙasa, da ta yi rashin nasara a hannun Atiku Abubakar na jam'iyyar PDP, a zaɓen shugaban ƙasar na ranar 25 ga watan Fabrairun 2023.
A kalamansa:
"Maƙiyan APC sun fara magana. Idan da ba Asiwaju Bola Ahmed Tinubu ba ne ya yi takara a zaɓen, da tun ƙarfe 12 na rana APC za ta sha kashi a hannun Atiku Abubakar na jam'iyyar PDP."
Sanusi Lamido Ya Yi Bayani Mai Daukar Hankali, Ya Bayyana Asarar Da Najeriya Ta Yi Na Rashin Zabar Osinbajo a Shugaban Kasa
Babban Lauya Ya Ba Wa APC Da Yan Najeriya Muhimmin Shawara
Rahoto ya zo kan yadda.wani babban lauya, ya bai wa jam'iyyar APC da ƴan Najeriyar muhimmiyar shawara kan shugabacin majalisar wakilai ta tarayya.
Frank Tiete ya haskowa jam'iyyar APC wanda ya fi dacewa ta ba ragamar shugabancin majalisar wakilai ta 10. Lauyan ya ce mataimakin kakakin majalisar na yanzu, ya fi dacewa da ɗarewa kan kujerar kakakin majalisar.
Asali: Legit.ng