APC Ta Nesanta Kanta Daga Ziyarar Da Tinubu Zai Kai Ribas
- Jam'iyyar APC reshen jihar Ribas ta nesanta kanta daga ziyarar da zababben shugaban kasa, Bola Tinubu zai kai jihar Ribas
- Tinubu zai kaddamar da wasu muhimman ayyuka da gwamnatin Nyesom Wike ta yi a jihar ta kudu
- APC a Ribas ta jaddada cewar bata rushe tsarinta don hadewa da gwamnan Ribas ba kamar yadda yake kokarin nunawa duniya a fakaice
Rivers - Jam'iyyar All Progressives Congress (APC) a jihar Ribas ta nesanta kanta daga ziyarar da zababben shugaban kasa, Bola Tinubu ke shirin kaiwa jihar mai albarkatun mai a ranar Laraba, rahoton Premium Times.
Tinubu wanda ya lashe zaben shugaban kasa na ranar 25 ga watan Afrilu karkashin inuwar APC zai kai ziyarar kwanaki biyu jihar don kaddamar da wata gadar sama da wani ginin kotu da gwamnatin Gwamna Wike ta gina.
Wike ya ayyana ranar Laraba, 3 ga watan Mayu a matsayin hutu, yana mai bukatar mutanen jihar da su fito kwansu da kwarkwata domin tarbar Tinubu, rahoton Channels TV.
Abun da APC ta ce game da ziyarar da Tinubu zai kai Ribas
A wata sanarwa da ya saki a ranar Talata, 2 ga watan Mayu, kakakin jam'iyyar APC a jihar, Darlington Nwauju, ya bayyana ziyarar a matsayin na gashin kai kuma bisa gayyatar Gwamna Wike. Ya kara da cewar bai da wata alaka da APC a jihar.
DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar
Nwauju ya ce:
"Muna kalubalantar gwamnana matsayinsa na gwamna mai barin gado (Mista Wike) da ya rage siyasa kawo rabuwar kai sannan ya janye daga dasa fitina tsakanin jam'iyyun adawa.
"Muna sane da cewar gwamnan na ta aiki tukuru don nunawa duniya cewar APC a jihar Ribas ta rushe tsarinta bayan ya sha nanatawa a hira da aka yi da shi a baya cewa ba zai taba yin hulda da jam'iyya mai kansa (APC) ba."
Bayan ya raba gari da dan takarar shugaban kasa na jam'iyyarsa ta PDP, Atiku Abubakar, sai gwamna Wike ya koma bayan Tinubu a zaben shugaban kasa.
A lokacin kamfen dinsa na shugaban kasa a jihar Ribas, Tinubu ya ziyarci Mista Wike a gidan gwamnati da ke Port Harcourt inda gwamnan ya bugi kirjin cewa yan takarar APC a jihar ba za su yi nasara a zaben ba sannan ya shawarci Tinubu a kan zuba jari a kansu (yan takarar APC).
Tambuwal ya yi sabbbin nade-nade makonni kafin mika mulki
A wnai labari na daban, mun ji cewa gwamnan jihar Sokoto, Aminu Tambuwal ya nada manyan sakatari 23 da daraktoci 15 yan makonni gabannin mika mulki ga sabuwar gwamnati.
Asali: Legit.ng