"Najeriya Ta Yi Babbar Asara Rashin Samun Osinbajo a Shugaban Kasa", Sanusi Lamido Sanusi

"Najeriya Ta Yi Babbar Asara Rashin Samun Osinbajo a Shugaban Kasa", Sanusi Lamido Sanusi

  • Tsohon sarkin Kano, Sanusi Lamido Sanusi ya ce Najeriya ta rashi samun Osinbajo a shugaban ƙasa
  • Sanusi ya yi nuni da cewa rashin samun Osinbajo a wannan matsayi, babbar asara ce ga Najeriya
  • Tsohon sarkin ya yi fatan ko da a nan gaba ne Najeriya ta samu sa'a Farfesa Osinbajo ya shugabance ta

Abuja - Tsohon sarkin Kano, Sanusi Lamido Sanusi, ya bayyana cewa Najeriya ta yi asarar rashin samun mataimakin shugaban ƙasa, Farfesa Yemi Osinbajo, a matsayin shugaban ƙasar nan.

Jaridar Vanguard ta kawo rahoto cewa, Sanusi ya bayyana hakan ne a wajen ƙaddamar da wani sabon littafi mai taken, “Osinbajo Strides: Defining Moments of an Innovative Leader,” a ranar Litinin.

Sanusi Lamido ya ce Najeriya asara rashin samun Osinbajo a shugaban kasa
Tsohon sarkin Kano, Sanusi Lamido Sanusi Hoto: Dailypost.com
Asali: UGC

A cewar tsohon gwamnan na babban bankin Najeriya, Najeriya ta yi asarar rashin zaɓen Osinbajo a matsayin shugaban ƙasar ta.

Kara karanta wannan

Zabin Tinubu a Shugabancin Majalisar Dattawa Ya Yi Kus-Kus da Shugaba Buhari, Bayanai Sun Bayyana

Sanusi ya ce rashin zaɓar Osinbajo a matsayin shugaban ƙasa ya sanya Najeriya ta yi babbar asara.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Ya yi nuni da cewa, Osinbajo yana ɗaya daga cikin muƙarraban wannan gwamnatin, waɗanda ke da muradin yin muhawara kan wane abu sannan ya samar da dalilai ƙwarara.

A kalamansa:

"Sannan na bugi ƙirji na faɗa cewa, dukkanin mu mun yarda cewa Najeriya ta yi asarar rashin samun mutum kamar sa (Osinbajo) a matsayin shugaban ƙasa, amma ina fatan cewa zai kasance a kusa domin hidimtawa ƙasar da bayar da shawarwari domin ganin cigaban ta."
"Lallai, ina da tabbacin zai yi hakan, a kowane matsayi ya samu kansa a nan gaba, sannan ƙila mu taki sa'a ya shugabance mu ko ya ɗauki ragamar wani jagoranci a matsayin dattijon ƙasa."

Sanusi ya bayyana cewa, saɓanin sauran ƴan siyasa, Osinbajo bai manta da abokanan sa ba bayan ya samu mulki, inda ya tabbatar masa da cewa abokan sa za su karɓe shi hannu biyo idan ya bar Villa, cewar rahoton Thisday.

Kara karanta wannan

To Fa: Kwamishinan Zaben Adamawa Ya Ƙara Shiga Sabon Tasku Kan Ayyana Aishatu Binani

Yaron Sanusi II Ya Fadi Ainihin Laifin Mahaifinsa da Ya Jawo Ganduje Ya Tsige Shi

A wani rahoton na daban kuma, kun ji yadda ɗan gidan Sanusi Lamido Sanusi, ya bayyana laifin da mahaifinsa ya yi, gwamna Ganduje ya tsige shi daga sarauta.

Sanusi II ya rasa sarautar Kano bayan gwamna Ganduje ya tumɓuke masa rawani.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng