Ko Sisin Kwabo Bar Karba Don Ayyana Aishatu Binani a Matsayin Gwamna Ba, Ari

Ko Sisin Kwabo Bar Karba Don Ayyana Aishatu Binani a Matsayin Gwamna Ba, Ari

  • Kwamishinan INEC na jihar Adamawa, Hudu Yunusa Ari, ya musanta raɗe-raɗin ya karbi cin hancin biliyan N2bn
  • Dakataccen kwamishinan ya ce ko kwandala bai karba ba kuma yana da hurumin sanar da sakamako a doka
  • Hudu, wanda rundunar yan sanda ke nema, ya ce a shirye yake ya miƙa kansa gaban kwamitin bincike

Adamawa - Kwamishinan zabe (REC) na jihar Adamawa, Barista Hudu Yunusa Ari, ya musanta jita-jitar ya karbi biliyan N2bn na goro domin ayyana Aishatu Binani a matsayin wacce ta lashe zaben gwamna.

Vanguard ta ce Barista Ari, ya ja hankalin yan Najeriya lokacin da ayyana sakamakon zaben gwamnan jihar Adamawa tun gabanin kammala tattara sakamako.

Hudu Yunusa Ari.
Ko Sisin Kwabo Bar Karba Don Ayyana Aishatu Binani a Matsayin Gwamna Ba, Ari Hoto: Bar. Hudu Yunusa Ari
Asali: UGC

kwamishinan hukumar zaɓen (INEC) wanda aka dakatar, ya ayyana Binani, yar takarar gwamna a inuwar APC, a matsayin zababbiyar gwamna duk da gwamna Fintiri na PDP ne a kan gaba.

Kara karanta wannan

'Yan Bindiga Sun Kaiwa Ayarin Gwamnan APC Kazamin Hari? Gaskiya Ta Bayyana

Sanata Aishatu Binani, yar takarar gwamnan APC a zaben 2023, ta kalubalanci Gwamna Ahmadu Umaru Fintiri na PDP, wanda daga baya INEC ta ayyana shi a matsayin wanda ya ci zaɓe a karo na biyu.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Ban yi dana sanin abinda na aikata ba - Hudu Ari

Da yake hira da BBC Hausa ranar Talata, Hudu ya ce ba ya nadamar komai game da ayyana sakamakon da ya yi ana tsaka da tattara sakamakon zabe a Adamawa.

Barista Hudu Yunusa Ari, dakataccen kwamishinam zaben da yan sanda suka gayyata, ya ce aikinsa ne sanar da sakamakon zabe kamar yadda doka ta tanada.

Yaushe zai gurfana gaban yan sanda?

Hudu ya kuma bayyana cewa ya shirya zuwa gaban yan sanda kan batun a wannan makon. Haka nan ya ce hukumar yan sanda ko DSS, ba wanda ya neme shi tun bayan abinda ya faru.

Kara karanta wannan

Binani ce ta ci zabe: Hudu Ari ya fasa kwai, ya ce manya a INEC sun karbi cin hanci daga Fintiri

A kalamansa, dakataccen kwamishinan zaɓen ya ce:

"Ban ce gwamna ya baiwa wani cin hanci ba, amma na san ana zargi. Na rantse da Allah, bani da wata alaƙa da Binani ko Fintiri. Wannan biliyan N2bn da aka ce an bani cin hanci ina zan kai su."
"Na sam haramun ne ka amshi kuɗi don ka taimaka wa wani, saboda haka zance ne na Soshiyal midiya amma ban karbi ko kwandala ba."

Yan Sandan Kasa Da Kasa Sun Gayyaci Kwamishinan Zaben Adamawa

A wani labarin kuma Rundunar yan sanda ta gayyaci Hudu Ari ya bayyana gaban kwamitin bincike don amsa tambayoyi

Barista Hudu Ari, wanda INEC ta dakatar daga matsayin kwamishinan zaben Adamawa, ya jawo cece kuce yayin cikon zaben gwamna a watan Afrilu.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262