Mun Shirya Mika Mulki Cikin Ruwan Sanyi, Ganduje Ya Maida Martani Ga NNPP
- Gwamnan jihar Kano, Abdullahi Ganduje, ya musanta ikirarin NNPP cewa gwamnatinsa na shirin zagon ƙasa a shirin miƙa mulki
- Ganduje, a wata sanarwa da kwamishinan yaɗa labarai ya fitar, ya ce gwamnati mai barin gado ta shirya miƙa mulki cikin ruwan sanyi
- Tun da fari, jam'iyyar NNPP mai kayan marmari ta yi ikirarin cewa Ganduje na zagon ƙasa a shirin miƙa mulki
Kano - Gwamnan jihar Kano, Dakta Abdullahi Umar Ganduje, ya ce gwamnatinsa ta shirya tsaf domin miƙa mulki ga sabuwar gwamnatin cikin ruwan sanyi ba tare da hayaniya ba.
Gwamnan ya faɗi haka ne a wata sanarwa da kwamishinan yaɗa labarai da harkokin cikin gida, Muhammad Garba, ya fitar, kamar yadda Channels tv ta rahoto.
Ya kuma musanta zargin da jam'iyyar NNPP ta yi cewa gwamnati mai barin gado na kulla makirci da zagon ƙasa a shrin miƙa mulki ga zababben gwamna, Abba Ƙabir Yusuf.
Kwamishinan ya ƙara da cewa tuni kwamitin miƙa mulki da sauran kananan kwamitoci a ma'aikatu da hukumomi suka maida hankali wajen shirin miƙa mulki lami lafiya.
DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka
Ya kuma yi bayanin cewa sun sanya wakilan sabuwar gwamnati a cikin kwamitin miƙa mulki ne domin tabbatar da gaskiya da yin komai a buɗe.
A ruwayar Vanguard, Garba ya ce:
"Manufar kafa kwamitim miƙa mulki shi ne ya shirya duk abinda ya kamata ya miƙa bayanai daga gwamnati mai barin gado zuwa sabuwar gwamnati ba tare nuna aƙida ba."
Ya yi kira ga wasu tsirarun mutane daga bangaren gwamnati mai zuwa da su san nauyin dake kansu, su maida hankali wurin tabbatar da an rabu cikin ruwan sanyi.
Bugu da ƙari, kwamishinan ya ce gwamnati mai barin gado ta yi tsammanin irin waɗannan akidoji da sabbin tsare-tsare daga NNPP amma duk saurin unguwar zoma ta bari a haihu, su bari a rantsar da sabuwar gwamnati.
NDLE Ta Faɗa Wa Kotu Gaskiya Kan Karar da PDP Ta Shigar da Tinubu
A wani labarin kuma Hukumar NDLEA ta yi bayani a gaban Kotu kan zargin Tinubu na da hannu a wata badakalar miyagun kwayoyi
A cewar hukumar, karar da jam'iyyar PDP ta shigar bata lokaci ne domin gwamnatin Amurka ba ta taɓa gurfanar da zababben shugaban ƙasa ba.
Ta ce ko da wasa ko a cikin rububi bata taba ganin sunan Tinubu a cikin sunayen masu laifi da ake taimakanni in taimakeka tsakanin Amurka da Najeriya.
Asali: Legit.ng