"Ku Hada Hannu da Tinubu," Lawan Ya Aike da Sako Ga Atiku da Obi
- Shugaban majalisar dattawa, Sanata Ahmad Lawan, ya ce ya zama tilas jam'iyyun adawa su gane cewa shugabanci na kowa ne
- Lawan ya roki fusatattun yan takarar shugaban kasa da su hakura su haɗa hannu da zababben shugaban ƙasa, Bola Tinubu
- Sanatan ya ce kawo ci gaba ga Najeriya ya fi muhimmanci fiye da cika burikan kai da kai
Abuja - Shugaban majalisar dattawa, Sanata Ahmad Lawan, ya roki manyan yan takarar da suka sha kaye, Atiku Abubakar na PDP da Peter Obi na LP, su haɗa hannu da zababben shugaban ƙasa, Bola Tinubu don ci gaban ƙasa.
Lawan ya yi wannan roko ne a Abuja ranar Jumu'a 28 ga watan Afrilu, 2023 yayin da ya karɓi bakuncin wakilan (OACPS) karkashin jagorancin Sakatare Janar, Georges Robelo Pinto Chikoti.
Yayin ganawa da wakilan, shugaban majalisar ya ce akwai bukatar jam'iyyun adawa su haɗa hannu da gwamnati mai zuwa wacce za'a rantsar rana 29 ga watan Mayu, 2023.
A ruwayar Daily Trust, Ahmad Lawan ya ce:
Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!
"Zabe ya riga da ya wuce, abinda ya rage shi ne tafiyar da shugabanci kuma shugabanci ai na kowa ne."
"Abinda ya zama wajibi kuma yake da matuƙar amfani a yau shi ne taya zamu haɗu wuri guda a matsayin mutanen ƙasa ɗaya ba tare da kallon banbancin siyasa ba, mu tabbatar mun kai ci gaban ƙasar mu mataki na gaba."
Lawan ya yaba wa ƙungiyar OACPS
Haka nan kuma Ahmad Lawan ya yaba wa shugaban ƙungiyar OACPS bisa manyan nasarorin da ya cimma da aiki tukuru wajen tabbatar da sauke nauyin da ya rataya a kan kungiyar.
Punch na rahoto Lawan na cewa:
"Muna kokarin kulla kawance da ƙungiyar tarayyar turai ba don komai ba sai don mu samu ikon dogaro da kanmu, maimakon a ko da yaushe mu nufe su da neman taimako."
A wani labarin kuma Kun Ji Cewa Gwamnan PDP Ya Naɗa Sabbin Sarakunan Gargajiya 149 a Jiharsa
Gwamna Udom Emmanuel na jam'iyyar PDP ya naɗa sarakunan gargajiya 149 a jihar Akwa Ibom ana sauran wata ɗaya tal ya bar mulki.
Gwamna ya naɗa wa mutanen rawanin Dagacin kauye da nufin kawo zaman lafiya mai ɗorewa da haɗin kai a tsakanin al'umma.
Asali: Legit.ng