Gwamna Wike Ya Gana da Tinubu a Abuja, Ya Fadi Kalamai Masu Jan Hankali

Gwamna Wike Ya Gana da Tinubu a Abuja, Ya Fadi Kalamai Masu Jan Hankali

  • Gwamnan jihar Ribas, Nyesom Wike, da rakiyar gwamnan Oyo, Seyi Makinde, sun gana da Bola Tinubu a Abuja
  • Wike, mamaban jam'iyyar PDP, ya bukaci yan Najeriya su jingine banbancin siyasa su marawa sabon shugaban ƙasa baya
  • A cewarsa, an kammala zaɓe kuma ya wuce, lokaci ya yi da kowa zai sanya kishin Najeriya a zuciya

Abuja - Gwamnan jihar Ribas, Nyesom Wike, tare da takwaransa na jihar Oyo, Seyi Makinde, sun ziyarci zababben shugaban ƙasa, Asiwaju Bola Ahmaed Tinubu a Defence House, Abuja.

Bayan ganawa da Tinubu, Gwamna Wike ya roki 'yan Najeriya su marawa sabon shugaban ƙasa baya, inda ya bayyana cewa lokacin siyasa ya ƙare.

Wike da Tinubu.
Gwamna Wike Ya Gana da Tinubu a Abuja, Ya Fadi Kalamai Masu Jan Hankali Hoto: channelstv
Asali: UGC

Channels TV ya haƙaito cewa Bola Tinubu, ɗan takarar shugaban ƙasa a inuwar APC, ya samu nasara kan manyan abokan hamayyarsa, Atiku Abubakar na PDP da Peter Obi na Labour Party.

Kara karanta wannan

Shugaba Buhari Ya Karbi Bakuncin Zababben Shugaban Kasa Tinubu, Hotuna Sun Bayyana

Tinubu, tsohon gwamnan jihar Legas, ya lallasa dukkan sauran yan takarar da suka gwabza a zaɓen shugaban ƙasa ranar 25 ga watan Fabrairu, 2023.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Gwamna Wike ya roki yan Najeriya

Sai dai duk da gwamna Wike ɗan jam'iyyar PDP ne bai goyi bayan ɗan takarar shugabsn kasa na jam'iyyarsa ba, hasali ma Tinubu ne ya samu kuri'u mafi rinjaye a jihar Ribas.

Jagoran jihar Ribas, Wike, ya yi kira ga ɗaukacin 'yan Najeriya da su goyi bayan sabuwar gwamnati wacce za'a rantsar ranar 29 ga watan Mayu, 2023.

Da yake hira da 'yan jaridar bayan kus-kus da Tinubu, Gwamna Wike ya ce:

"Zabe ya zo kuma ya wuce, an bayyana wanda ya samu nasara, don haka ya zama wajibi kan kowane ɗan Najeriya ya mara masa baya domin ƙasar mu ta yi kyau."

Kara karanta wannan

Ta Fasu An Ji: Zababɓen Shugaban Ƙasa, Bola Tinubu, Ya Gana da Wasu Gwamnoni da Sarkin Kano

"Ina da kwarin guiwa cewa (zababben shugaban kasar nan) yana da duk abinda ake buƙata na kawo sauyi mai kyau."

Buhari da Tinubu sun yi sallar Jummu'a tare

A wani labarin kuma Shugaba Buhari Ya Karbi Bakuncin Zababben Shugaban Kasa, Bola Tinubu a Aso Villa

Shugaban ƙasa mai barin gado, Muhammadu Buhari ya karbi bakuncin zababben shugaban kasa, Alhaji Ahmed Bola Tinubu a fadarsa da ke Abuja

Buhari da Tinubu sun yi Sallar Jumu'a tare yau a fadar shugaban kasa amma babu wanda ya zanta da manema labarai.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262