Sabuwar Rigima Ta Kunno Jam'iyyar APC, 'Yan Takarar Gwamna Na Neman Kotu Ta Soke Zaben Fidda Gwanin Gwamna
- Sabuwar rigima ta kunno kai a jami'iyyar All Progressives Congress (APC) a jihar Kogi kan zaɓen fidda gwanin gwamna
- Biyu daga cikin ƴan takarar da suka yi rashin nasara a zaɓen fidda gwanin sun garzaya kotu, suna ƙalubalantar sa
- Sun garzaya kotun ne dai da buƙatar ta soke shi saboda a cewar su, zaɓen fidda gwanin haramtacce ne
Jihar Kogi - Biyu daga cikin ƴan takarar zaɓen fidda gwanin gwamnan jihar Kogi, na jam'iyyar All Progressives Congress (APC), sun garzaya babbar kotun tarayya a Abuja neman a soke zaɓen.
Jaridar Daily Trust ta tattaro cewa, Sanata Smart Adeyemi da ɗan tsohon gwamnan jihar, Shuaibu Abubakar Audu, na neman babbar kotun tarayyar ta soke zaɓen fidda gwanin gwamna da APC ta yi a jihar.
Bayan waɗannan mutum biyun, sauran ƴan takarar da suka garzaya kotu suna ƙalubalantar zaɓen sun haɗa da, tsohon ƙaramin ministan ilmi, Farfesa Stephen Ocheni, mataimakin kakakin APC na ƙasa, Murtala Yakubu Ajaka da Dr Sanusi Ohiara.
A cikin ƙararrakin na su masu lambobin FHC/ABJ/CS/556/2023 da FHC/ABJ/ CS/557/2023, Adeyemi da Audu suna neman kotun ta ayyaɓa zaɓen fidda gwanin na APC a matsayin haramtacce, wanda ya saɓa doka.
DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka
Fusatattun ƴan takarar gwamnan sun yi zargin gwamnan jihar Yahaya Bello, ya zaɓi ɗan takarar da ya ke so, Usman Ododo, wanda hakan ya saɓa wa sashi na 177 da kundin tsarin mulkin ƙasar nan, da sashi na 29 da 84 na sabuwar dokar zaɓe da sakin layi na 20 na kundin tsarin mulkin APC.
Suna kuma neman kotun ta bayar da umurnin tilasta hukumar INEC ƙin amincewa da Usman Ododo a matsayin ɗan takarar gwamnan jam'iyyar APC a jihar, bisa dalilin yin ba daidai ba a zaɓen fidda gwanin, cewar Premium Times.
Haka kuma, ƴan takarar sun buƙaci kotu da ta tilastawa jam'iyyar APC sake sabon zaɓen fidda gwani, wanda kowane ɗan takara zai fafata a cikin sa ba tare da nuna fifiko kan wani ba.
Tinubu Ya Bayyana Zabin Sa a Shugabancin Majalisar Dattawa
A wani rahoton na daban kuma, kun ji cewa, zaɓaɓɓen shugaban ƙasa, Bola Tinubu ya bayyana waɗanda ya ke son su shugabanci majalisar dattawa ta 10.
Tinubu ya zaɓi Sanata Godswill Akpabio da wani sanata a Arewacin Najeriya a matsayin waɗanda ya ke so, su shugabanci majalisar dattawan.
Asali: Legit.ng