Bola Tinubu Ya Gana da Gwamnonin APC da Sarkin Kano a Abuja
- Zababben shugaban ƙasa, Alhaji Bola Ahmed Tinubu, ya karbi bakuncin gwamnonin jam'iyyar APC a gidansa na Abuja
- Tinubu, wanda bai jima da dawowa Najeriya ba, ya kuma gana da Sarkin Kano, Alhaji Aminu Bayero CFR
- Gwamna Atiku Bagudu ya ce sun je kara taya Tinubu murnar lashe zabe da kuma yi masa barka da dawowa gida Najeriya
Abuja - Shugaban ƙasa mai jiran gado, Asiwaju Bola Ahmed Tinubu, ya gana da gwamnonin jam'iyyarsa ta APC a gidan da aka ware masa a birnin tarayya Abuja.
Wannan gana wa da manyan kusoshin jam'iyya mai mulki ta zo ne kwanaki kaɗan bayan zababben shugaban kasan ya dawo gida Najeriya daga Faransa, inda ya shafe kusan wata guda.
A wata sanarwa da ya wallafa a shafinsa na Tuwita ranar Alhamis da daddare, Bola Tinubu ya ce ya gana da Sarkin Kano, Alhaji Aminu Ado Bayero a Abuja, sun tattauna batutuwa.
"Da safiyar yau, zababben mataimakin shugaban ƙasa ya haɗu da ni muka karɓi bakuncin mambobin ƙungiyar gwamnonin ci gaba karkashin jagorancin Atiku Bagudu na Kebbi a gidana da ke Abuja."
DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar
"Wannan ya biyo bayan ganawar abokai kuma wanda na fi jin daɗinta tare da Sarkin Kano, Alhaji Aminu Bayero CFR."
- Bola Ahmed Tinubu.
Meyasa gwamnonin APC suka kaiwa Tinubu ziyara a Abuja?
Da yake zantawa da manema labarai jim kaɗan bayan ganawarsu da Tinubu, shugaban ƙungiyar gwamnonin APC kuma gwamnan Kebbi, Atiku Bagudu, ya ce sun je taya zababben shugaban kasa murnar samun nasara a zaben 2023.
Gwamna Bagudu ya kara da cewa sun kuma yi wa Bola Tinubu barka da dawowa bayan tafiyar da ya yi zuwa kasar Turai inda ya shafe kusan wata guda.
A ranar 29 ga watan Mayu, 2023, za'a rantsar da Tinubu a matsayin sabon shugaban ƙasa a Najeriya bayan lashe babban zaɓen 25 ga watan Fabrairu, 2023.
Wata 6 zan yi a Daura - Buhari
A wani labarin kuma Shugaban Ƙasa, Muhammadu Buhari, ya ce ba zai jima ba a Daura, zai koma Kaduna bayan sauka da kan karagar mulki
Buhari, wanda wa'adin zangon mulkinsa na biyu zai kare ranar 29 ga watan Mayu, 2023, ya jima yana cewa ya ƙagara ya koma Daura mahaifarsa.
Amma yayin da ya karɓi bakuncin gwamnonin APC a Aso Villa, Buhari ya ce watanni 6 kaɗai zai yi a Daura, jihar Katsina.
Asali: Legit.ng