Atiku Ya Ɓallo Wa Tinubu Ruwa Da Ka Iya Hana Rantsar Da Shi A Ranar 29 Ga Watan Mayu
- Atiku bai sassauta kan kudirin kwatar nasararsa daga hannun Tinubu a kotun kararrakin zabe ba
- A sabuwar karar da Atiku ya shigar gaban kotun da ke Abuja, ya zargi Tinubu da kasancewa dan kasashe biyu
- Ya bayyana cewa Tinubu ya mallaki Fasfo din Najeriya da Guinea a lokaci guda, wanda hakan ya saba da dokokin zabe
FCT, Abuja - An zargi zababben shugaban Najeriya, Asiwaju Bola Ahmed Tinubu, da kasancewa dan kasar Guinea da Najeriya.
Babban abokin hamayyarsa Atiku Abubakar ne ya bayyana haka a wata sabuwar kara da ya shigar gaban kotun sauraron kararrakin zaben shugaban kasa kan zaben 2023.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Kamar yadda jaridar PM News ta ruwaito, takardar karar ta kalubalanci Tinubu bisa rashin bin dokar hukumar zabe INEC da ta bukaci ya gabatar da cikakkun takardun shaidarsa a takardar EC9 kamar yadda doka ta tanada.
Shugaban tawagar lauyoyin Atiku Chris Uche (SAN), ya ce Tinubu ba shi da damar tsayawa takarar shugabancin kasa idan ana bin dokokin da kundin tsarin mulkin kasa ya shimfida.
Atiku ya zargi Tinubu da aikata laifukan da suka shafi safarar kwayoyi
A wata bangaren karar, Atiku ya bayyana cewa Tinubu ba shi da ingancin tsaya wa takarar shugabancin kasa saboda zarginsa da aikata laifukan da suka shafi miyagun kwayoyi a kasar Amurka.
Karar ta cigaba cewa laifin ya janyo Tinubu ya yi asarar dalar Amurka 460,000 a matsayin kudin yarjejeniya, Business Day ta ruwaito.
A martanin da suka yi, masu kare Tinubu
"Batun hada wanda ake kara na biyu (Tinubu) da mai kara na farko (Atiku) wanda ya rike matsayin mataimakin shugaban kasa na shekara takwas ba shi da makama."
Atiku, a nasa bangaren, ya ce nasarar Tinubu a zaben shugaban kasa ba ta inganta ba saboda bai cika sharuddan da za su bayyana shi a matsayin wanda ya lashe zabe ba.
Tsohon mataimakin shugaban kasar ya bayyana nasarar Tinubu a matsayin cikas ga yancin masu kada kuri'a na zabar shugaban da ya cacanta.
Ya ce Tinubu bai samu kaso 25 na kuri'un da aka kada a birnin tarayya Abuja ba, wanda ya na cikin sharadi.
Asali: Legit.ng