Manufofin Tinubu Sun Nuna Za'ai Zaman Doya da Manja Tsakaninsa da Buhari, Hadimin Atiku

Manufofin Tinubu Sun Nuna Za'ai Zaman Doya da Manja Tsakaninsa da Buhari, Hadimin Atiku

  • Hadimin tsohon mataimakin shugaban ƙasa, Atiku Abubakar, ya yi hasashen cewa alaƙa zata yi tsami tsakanin Tinubu da Buhari
  • Daniel Bwala ya ce manufofin zaɓaɓɓen shugaban kasa sun nuna karara zai yaƙi shugaba Buhari idan ya hau mulki
  • Tsawon shekara 8 da Buhari ya yi a kan madafun iko, yana yawan ɗora laifin taɓarɓarewar kasar nna kan PDP

Abuja - Daniel Bwala, mai magana da yawun ɗan takarar shugaban ƙasa a inuwar PDP, Atiku Abubakar, ya ce da yuwuwar a yi zaman doya da manja tsakanin Bola Tinubu da shugaba Buhari.

Mista Bwala ya yi ikirarin cewa manufofin zababben shugaban ƙasa, Bola Ahmed Tinubu, sun nuna cewa zai yaƙi shugaban ƙasa, Muhammadu Buhari, nan gaba.

Buhari da Bola Ahmed Tinubu.
Shugaba Muhammadu Buhari tare da Bola Tinubu Hoto: Buhari Sallau
Asali: UGC

Hadimin Atiku ya yi wannan ikirarin ne a wani rubutu da ya wallafa a shafinsa na Tuwita ranar Laraba 26 ga watan Afrilu, 2023.

Kara karanta wannan

Somin-tabi: Bidiyon lokacin da Tinubu da Shettima ke kaura zuwa gidan gwamnati

A cewarsa, manufofin da Asiwaju Tinubu ya tasa gaba sun nuna da yuwuwar ya ɗaga wa shugaba Muhammadu Buhari yatsa kan wasu tsarukan gwamnatinsa.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Bwala ya tuna yadda shugaba Buhari ya zargi gwamnatin jam'iyyar PDP da ta gabata kafin zuwansa, inda ya ɗora mata laifin lalata ƙasar nan.

Kakakin tsohon mataimakin shugabaan kasan ya ce abun zai daɗin kallo da sha'awa lokacin da gwamnatin Bola Ahmed Tinubu zata fito ta fara kirkiro na ta uzurin da zata baiwa 'yan Najeriya.

A rubutun da ya wallafa Daniel Bwala ya ce:

"Abun zai ƙayatar kuma ya ba da sha'awa lokacin da zamu fara jin uzuri ya fara fito wa daga wurinsu saboda za'a gamu da tulin uzuri nan gaba."
"Gwamnatin yanzu da ke gab da sauka, tsawon shekara Takwas da ta kwashe kan madafun iko bata da aiki sai rataya laifin gazawarta kan jam'iyyar PDP."

Kara karanta wannan

Karin Bayani: Fitaccen Attajirin Da Ya Fi Kowa Kuɗi a Afirka Ya Kaiwa Tinubu Ziyara, Hotuna Sun Bayyana

"(Shugaban ƙasa) Na gaba wa zai ɗora wa laifi? Saboda baki ɗaya manufofinsa sun kama hanyar yaƙar magabacinsa."

Bola Tinubu Zai Kaddamar da Wasu Manyan Ayyuka a Jihar Ribas

A wani labarin kuma Gwamna Wike ya tabbatar da ranakun zuwan Bola Ahmed Tinubu jihar Ribas domin kaddamar wasu manyan ayyuka 2.

Gwamnan jihar Ribas, Nyesom Wike, kuma jagoran gwamnonin G-5 na PDP, ya ce zababben shugaban ƙasa zai kai musu ziyara ya kwana biyu a watan Mayu.

Jihar Ribas na ɗaya daga cikin jihohi 12 da Bola Tinubu ya samu kuri'u mafi rinjaye a zaben shugaban kasan da aka kammala a watan Fabrairu.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262