Faduwa Zabe: Atiku Ya Yi Wa Tinubu Gori A Martanin Da Ya Mayar Masa
- Alhaji Atiku Abubakar ya mayar da martani ga Asiwaju Bola Tinubu, zababben shugaban kasar Najeriya kan kiransa 'wanda ya saba fadi zabe'
- Dan takarar shugaban kasar na PDP ya ce gara shi takarar zabe ya rika yi tun 1993 amma ba a taba alakanta shi da kwaya ba ko rudani a takardunsa
- A halin yanzu Atiku wanda ya zo na biyu a zaben shugaban kasa na 2023 yana kotun karar zabe don kallubalantar nasarar Bola Tinubu
Atiku Abubakar, dan takarar shugaban kasa na jam'iyyar PDP ya ce shi ba kamar Bola Tinubu bane, zababben shugaban kasa, wanda takararsa ke cike da abubuwa masu rudani, Daily Trust ta rahoto.
An ayyana Tinubu a matsayin wanda ya lashe zaben ranar 25 ga watan Fabrairu da kuri'u 8,794,726.
Abubakar ya samu kuri'u 6,984,520 yayin da Peter Obi na jam'iyyar Labour ya zo na uku da kuri'u 6,101,533.
Amma, dan takarar na PDP yana kallubalantar nasarar Tinubu a kotun karar zabe.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
A takardar kara mai lamba CA/PEPC/05/2023, Atiku da PDP ta yi zarge-zarge da dama ciki har da zargin cewa Tinubu bai cancanci shiga zaben ba, The Cable ta rahoto.
A jawabin farko na nuna rashin amincewa da karar, Tinubu ya bayyana tsohon mataimakin shugaban kasar a matsayin wanda ya saba shan kaye "da ke takarar shugaban kasa tun 1993 yana shan kaye, ko a matakin zaben fidda gwani ko babban zabe."
Martanin Atiku
Da ya ke mayar da martani ga Tinubu, Atiku ya amsa cewa ya sha yin takarar shugaban kasa tun 1993, amma ba shi da "alaka da kwaya".
Abubakar ya ce:
"Mai shigar da kara na farko, akasin wanda aka yi kara na biyu (Tinubu), ya dade yana takarar shugaban kasa, duba da cewa ba shi da alaka da kwaya, babu rudani game da shekarunsa, haihuwarsa, jiharsa ta asali, jinsi, takardun karatu, lafiya, ayyuka, zamansa dan kasa da duk wasu batutuwa da suka shafi tanadin doka kan takarar ofishin shugaban kasar Najeriya."
Ya ce zababben shugaban kasar ya bada:
"Mabanbantan bayanai dangane da ainihin ranar haihuwarsa, makarantun sakandare da ya yi (Kwalejin Gwamnati ta Ibadan); ainihin jiharsa, jinsi, ainihin sunansa; takardun shaidan karatun jami'a (Jami'ar Jihar Chicago)."
"Digirin din da wanda aka yi karar na biyu ya ce ya samu daga Jami'ar Jihar Chicago ba tasa bane amma na wata mace da aka nuna alama da (F) a satifiket mai dauke da sunan Bola Tinubu.
"Wanda aka yi karar na biyu bai bayyanawa wanda aka yi kara na farko (INEC) cewa yana da fasfo din zama dan kasar Guinea ba mai lamba D00001551, baya ga kasancewarsa dan Najeriya. An bukaci wanda aka yi karar na biyu ya kawo kwafin fasfo din biyu."
Dan takarar na PDP ya kara da cewa:
"An taba kwace $460,000 daga wurin Tinubu saboda laifi mai alaka da kwayoyi a gaban mai shari'a John A Nordberg na Amurka, a asusun bankin First Heritage mai lamba 263226700 na wanda ake zargin na biyu kasancewarsa kudi na safarar kwaya wanda ya saba sashi na 18 U.S.C. 1956 da 1947 na laifuka masu alaka da kwayoyi."
A bangare guda, Atiku ya yi garambawul a tawagar lauyoyinsa ya nada Chris Uche jagoranci, ya karba daga hannun Joe Gadzama.
Asali: Legit.ng