Babu Abun da Zai Hana Rantsar Da Tinubu a Ranar 29 Ga Watan Mayu, Sai Allah - Keyamo

Babu Abun da Zai Hana Rantsar Da Tinubu a Ranar 29 Ga Watan Mayu, Sai Allah - Keyamo

  • Festus Keyamo, karamin ministan kwadago ya magantu a kan shirin rantsar da zababben shugaban kasa, Bola Tinubu
  • Keyamo ya nanata cewa babu abun da zai hana rantsar da Tinubu a matsayin shugaban kasa a ranar 29 ga watan Mayu
  • A cewarsa Allah ne kadai zai iya hana tabbatar da hakan amma ba wani wani dalili da ya danganci doka ba

Karamin ministan kwadago da daukar ma'aikata, Festus Keyamo ya ce Allah ne kadai zai iya hana rantsar da zababben shugaban kasa, Asiwaju Bola Tinubu a ranar 29 ga watan Mayu.

Keyamo ya bayyana wannan hasashen ne a cikin wata sanarwa a ranar Talata, 25 ga watan Mayu, jaridar Vanguard ta rahoto.

Zababben shugaban kasa, Bola Tinubu
Babu Abun da Zai Hana Rantsar Da Tinubu a Ranar 29 Ga Watan Mayu, Sai Allah - Keyamo Hoto: @officialABAT
Asali: Twitter

Kakakin rusasshiyar kwamitin na yakin neman zaben shugabancin Tinubu-Shettima, ya ce jam'iyyar All Progressives Congress (APC) mai mulki bata tattare da kowani fargama dangane da bikin rantsar da Tinubu.

Kara karanta wannan

Ahaf: Sirri ya fito, an fadi gaskiyar alakar Tinubu da kasancewarsa dan kasar Guinea

Ya kara da cewar kowani dan adawa da ke tunanin ba za a rantsar da Tinubu a matsayin shugaban kasa ba a ranar 29 ga watan Mayu saboda dalilai na doka toh yana shashantar da kansa ne.

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

Ya kamata masu adawa su fara shiri kan zaben 2027, Keyamo

Da yake magana game da dawowar Tinubu kasar bayan hutun makonni hudu da ya yi a Faransa, Keyamo ya kuma shawarci yan adawa da su mayar da hankali a kan kararrakinsu da ke kotu ko su fara shiri kan babban zaben 2027.

Keyamo ya ce:

"Me zai sa a shiga kowani fargaba? Duk wani dan adawa da ke raye a yanzu wanda ya yarda cewa wasu dalilai na doka za su sa a ki rantsar da Asiwaju toh lallai mafarki yake yi.
"Sai dai idan akwai wani nufi na Allah wanda shine madaukakin sarki, babu abun da zai hana rantsar da Asiwaju. Ya kamata yan adawa su mayar da hankali kan kararrakinsu a kotu ko su fara shirye-shiryen 2027."

Kara karanta wannan

Atiku, Tinubu, Obi: Satguru Maharaj Ji Ya Bada Sabuwar 'Wahayi' Game Da Makomar Zaben 2023

Haka kuma, Keyamo ya ce y ji dadin kallon wasannin barkwancin da aka dunga yi a kan baranbaramar ubangidan nata, Tinubu a lokacin yakin neman zabe.

Ya ce yayin da masu barkwancin suka mayar da hankali wajen zuzuta baranbaramar, su sun mayar da hankali wajen yin kamfen ba ji ba gani kuma wanka ta biya kudin sabulu, rahoton Peoples Gazatte.

Tsohon dan takarar shugaban kasa ya nemi kotu ta dakatar da rantsar da Tinubu

A wani labarin kuma, mun ji cewa wani tsohon dan takarar shugaban kasa a zaben 2019, Ambrose Owuru, ya bukaci kotun daukaka kara da ta hana rantsar da zababben shugaban kasa, Bola Tinubu a ranar 29 ga watan Mayu.

A cewar Owuru, shine ya lashe zaben 2019 amma bai samu yin wa'adinsa ba saboda fin karfi da aka yi masa ta hanyar ba Shugaban Kasa Muhammadu Buhari wa'adinsa.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Musa avatar

Aisha Musa (Hausa writer) Aisha Musa 'yar jarida ce wacce ta kwashe shekaru biyar tana aikin gogewa a harkar yada labarai. Ta kammala karatun ta a Jami'ar Ibrahim Badamasi Babangida (IBB Lapai) a shekarar 2014 tare da digirin farko a fannin Tarihi. Aisha Editan Hausa ce wacce ke amfani da kwarewa da kwazonta don karfafawa wasu gwiwar yin aiki tukuru don cimma nasara. Ta karbi lambar yabo na gwarzuwar shekarar 2021 a bangaren Hausa na Legit. Za ku iya aika mata sakonnin imel ta adireshinta aisha.musa@corp.legit.ng