Mutanena Suka Ci Amana, Suka Taimaka Wa Bola Tinubu A Boye, In Ji ‘Dan Takaran 2023
- Adewole Ebenezer Adebayo ya zargi wasu daga cikin ‘yan tafiyarsa da yaudarar jam’iyyarsu ta SDP
- ‘Dan takaran Shugaban kasar ya ce mutanensa sun rika sulalewa, su na komawa wajen su Bola Tinubu
- Adebayo yana da ra’ayin cewa APC tayi nasara a 2023 ne saboda ta na da kwararrun ‘yan siyasa
Abuja - Adewole Ebenezer Adebayo ne ‘dan takaran da ya tsayawa jam’iyyar SDP a zaban shugaban kasa, ya koka a kan yadda abubuwa suka kasance a 2023.
Da aka zanta da shi a wata doguwar hira, Adewole Ebenezer Adebayo ya shaidawa Vanguard cewa ya samu matsala a zaben 2023, tun daga wajen magoya baya.
Adewole Adebayo yake cewa an ci amanarsa a zaben na 2023 kamar yadda Judas ya yi wa Yesu.
‘Dan siyasar ya ce ba komai ya jawo Asiwaju Bola Ahmed Tinubu ya yi galaba a kan shi da sauran ‘yan takara ba sai saboda yana tare da kwararrun ‘yan siyasa.
Tinubu zai dare mulki
Duk da jam’iyyun LP da PDP sun shigar da kara, a matsayinsa na Lauya, ‘dan takaran na SDP ya ce Atiku Abubakar da Peter Obi ba za su yi nasara a kotu ba.
DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar
Adebayo ya nuna babu ta yadda jam’iyyar PDP za ta iya lashe zaben bana tun farko domin siyasar kudi ta saba yi, sannan an wuce da yayin Atiku Abubakar.
A tattaunawar da aka yi da shi, ‘dan takaran ya yi bayanin abin da ya hana shi zuwa kotu, har aka ji ya fito yana mai taya ‘dan takaran APC murnar lashe zabe.
Barnar da aka yi wa SDP
Alal misali a Jigawa, duk abin da na yi, sai Gwamnan ya zo ya ruguza shiri na. Ba na tunanin Tinubu ya san abin da nake yi, Gwamnan ya hana ni sakat.
A duk lokacin da nayi kokarin yin wani katabus a Jigawa, a karshe sai dai in ji labari mara dadi.
Idan mutum yana tare da na ni, kafin ka ce ‘kobo’, sai in ji wannan mutumi ya sauya sheka zuwa jam’iyyar APC, kamar wani Sanata da jigo ne a kamfe dina.
Ana zaune kurum ya shaidawa Duniya ya koma jam’iyyar APC, ya yi watsi da takarar Sanatansa.
- Adewole Ebenezer Adebayo
Shirin karbar mulki
A baya an samu rahoto cewa kanin Marigayi Shugaba Umaru ‘Yar’adua, Abdulaziz 'Yar'adua ya samu shiga cikin Kwamitin taya Bola Tinubu karbar mulki.
An bada sunayen Abubakar Kyari wanda mutumin Kashim Shettima ne da wani tsohon ‘Dan takaran Gwamna a Ekiti da Mai dakin Janar Buba Marwa.
Asali: Legit.ng