Rigima Sabuwa Wata Jam'iyya Ta Garzaya Kotu Neman a Hana Rantsar Da Tinubu Matsayin Shugaban Ƙasa
- Wata sabuwar barazana ta kunno kai dangane da rantsar da Tinubu a matsayin sabon shugaban ƙasa
- Jam'iyyar Hope Democratic Partt (HDP) da ɗan takarar shugaban ƙasar a 2019 sun shigar da ƙara kan rantsar da Tinubu
- A ƙarar ta su, suna neman kotu ta hana shugaba Buhari rantsar da zaɓaɓɓen shugaban ƙasar a matsayin magajin sa
Abuja - An shigar da wata sabuwar ƙara a kotun ɗaukaka ƙara da ke birnin tarayya Abuja, domin hana rantsar da Asiwaju Bola Ahmed Tinubu, a matsayin sabon shugaban ƙasa a ranar 29 ga watan Mayun 2023.
Ƙarar mai lamba CA/CV/259/2023 wacce ɗan takarar jam'iyyar Hope Democratic Party (HDP), Cif Ambrose Albert Owuru, ya shigar tana neman kotun ta bayar da umurni a hana rantsuwar, rahoton Leadership ya tabbatar.
Jam'iyyar tana neman kotun ta hana shugaban ƙasa Muhammadu Buhari, Antoni Janar na tarayya da hukumar zaɓe mai zaman kanta (INEC), daga rantsar da zaɓaɓɓen shugaban ƙasar a ranar 29 ga watan Mayun 2023.
Jam'iyyar ta fafata a zaɓen shugaban ƙasa na shekarar 2019, sannan a yanzu tana son shugaba Buhari da AGF da INEC su dakata da ɗaukar wani mataki dangane da zaɓen 2023 wanda ya samar da Tinubu a matsayin shugaban ƙasa, cewar rahoton Daily Post
Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!
Owuru, wanda ya ke iƙirarin cewa shine a bisa tanadin kundin mulki wanda ya lashe zaɓwn shugaban ƙasa na shekarar 2019, ya haƙiƙance cewa kada a rantsar da Tinubu ko wani magajin shugaba Buhari, tun da shine kundin tsarin mulki ya yarda ya lashe zaɓen 2019 kuma bai yi wa'adin sa ba kamar yadda doka ta tanada.
Daga cikin abinda ya ke nema, Owuru ya haƙiƙance cewa shugaba Buhari ya yi masa kwacen mulki tun shekarar 2019 saboda kotun koli ba ta yanke hukunci kan ƙarar da ya shigar ba yana ƙalubalantar bayyana Buhari a matsayin wanda ya lashe zaɓen.
Amsar Mulki: Bayan Kwashe Kwanaki a Kasar Waje, Daga Karshe An Bayyana Ranar Da Bola Tinubu Zai Dawo Najeriya
Waɗanda aka lissafo a cikin ƙarar sune shugaban ƙasa Muhammadu Buhari, Antoni Janar na tarayya (AGF) da hukumar INEC.
Ƙarar wacce Mr Odion Peter ya shigar tuni har an aikewa shugaba Buhari da Antoni Janar na tarayya ta hannun lauyoyin su Mrs Maimuna Lami Ashiru ta ministirin shari'a, yayin da aka miƙa ta hukumar INEC a hannun shugaban sashin shari'a na hukumar, Mr S. O Ibrahim (SAN).
An bar APC da ciwon kai, mutanen Arewa maso yamma sun huro wuta
A wani rahoton na daban kuma, mutanen yankin Arwwa.maso Yamma na ci gaba da matsin lamba kan samun shugabancin majalisar dattawa ta 10.
Mutanen yankin sun haƙiƙance cewa yanzu lokacin mayar da biki ne duba da irin ruwan ƙuri'un da suka yiwa APC a zaɓen shugaban ƙasa.
Asali: Legit.ng