Da Yuwuwar Atiku Ya Samu Nasara Kan Tinubu a Kotu, Olarewaju
- Sabon hasashe kan hukuncin da Kotu zata yanke kan karar zaɓen shugaban ƙasa 2023 da aka shigar gabanta ya bayyana
- Demola Olarewaju, hadimin tsohon mataimakin shugaban ƙasa, Atiku Abubakar, ya faɗi abinda yake hange kan shari'ar da ke gaban Kotu
- Ya ce Ubangidansa ya haɗa kwararan hujjojin da zasu ɗora shi kan Tinubu a Kotu, kuma akwai yuwuwar canja zaɓe
Ƙorafe-ƙorafe kan zaɓen shugaban kasan da aka kammala a Najeriya na neman dawowa ɗanye yayin da aka fara hasashen hukuncin da mai yuwuwa Kotu zata yanke kan karar da ke gabanta.
Idan zaku iya tunawa, ɗan takarar shugaban kasa a inuwar PDP, Atiku Abubakar, da takwaransa na Labour Party, Peter Obi, sun shigar da ƙara kan zababben shugaban ƙasa, Bola Tinubu, da INEC.
Babban abinda suka yi musu a gaban Kotu shi ne gazawar INEC ta bayyana sakamakon zaben a yanar gizo a lokacin da ya dace da kuma rashin gamsuwa da aikin na'urar BVAS.
Magana Ta Ƙare: Daga Dawowa Gida, Tinubu Ya Faɗi Gaskiya Kan Rashin Lafiyarsa, Ya Aike da Saƙo Ga Yan Najeriya
Demola Olarewaju, mashawarci na musamman kan harkokin midiya ta zamani ga Atiku Abubakar, ya ce ubangidansa ne ya ci zaɓe babu tababa.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
A wani rubutu da ya wallafa a shafinsa na Tuwita kuma Legit.ng Hausa ta ci karo da shi, Olarewaju ya ce:
"Akwai miloyoyin dalilan gazawa amma ɗaya tal muke buƙata mu ci nasara kuma Atiku Abubakar, na da wannan dalili a 2023. Wannan ne abinda ya sa ya lashe zaɓe, muna da Hujja mai ƙarfi."
Ya ƙara da cewa hujjojin da ke gaban jam'iyyar PDP da tawagar lauyoyi sun isa su kwato wa Atiku haƙƙinsa na zama zababben shugaban ƙasa.
Mista Olarewaju ya ce mafi karancin abinda Kotu zata yanke shi ne a canza zaɓe tsakanin Atiku da wani ɗan takara wanda Kotun kaɗai zata bayyana shi.
APC ta ƙara karfi a kudu
A wani labarin kuma 'Yan Majalisar Tarayya 3 Da Dubbannin Mambobi Sun Sauya Sheƙa Zuwa APC
Kwana 1 da dawowar shugaban kasa mai jiran gado, Bola Tinubu, wasu yan majalisar tarayya uku sun koma APC a jihar Imo. Yan majalisar na PDP da APGA sun sauya sheka tare da magoya baya sama da 2000. Sun faɗi babban abinda ya ja hankalinsu suka shiga APC mai mulki a yanzu.
Asali: Legit.ng