Yan Majalisar Tarayya Uku Sun Sauya Sheƙa Zuwa APC a Jihar Imo

Yan Majalisar Tarayya Uku Sun Sauya Sheƙa Zuwa APC a Jihar Imo

  • 'Yan majalisar wakilan tarayya uku da dubannin magoya bayansu sun sauya sheka zuwa jam'iyyar APC a jihar Imo
  • A wurin taron da aka shirya don tarbansu a Owerri, 'yan majalisun daga PDP da APGA sun sha alwashin goyon bayan gwamna Uzodinma
  • Shugaban APC na jihar ya yaba da matakin da suka ɗauka kana ya miƙa musu tutar jam'iyya a wurin taron

Imo - Mambobin majalisar wakilan tarayya 3 da ke kan kujera a inuwar jam'iyyar PDP da APGA a jihar Imo, kudu maso gabashin Najeriya sun sauya sheka zuwa APC mai mulki.

Channels tv ta tattaro cewa 'yan majalisun sun sauya sheƙa zuwa jam'iyya mai mulki tare da magoya bayansu kusan mutane 2,000.

Siyasar jihar Imo.
Yan Majalisar Tarayya Uku Sun Sauya Sheƙa Zuwa APC a Jihar Imo Hoto: channelstv
Asali: UGC

Yan majalisar wakilan tarayya da suka ɗauki wannan mataki sun ƙunshi Bede Eke, mai wakiltar mazaɓar Aboh Mbaise/Ngor Okpala, a inuwar PDP, da Emeka Nwawuba na APGA mai wakiltar Mbaitoli/Ikeduru.

Kara karanta wannan

Da Ɗumi-Ɗumi: An Yi Babban Rashi, 'Yan Bindiga Sun Kashe Shugaban Jam'iyya da Wasu Mutum 3

Sai kuma ɗan majalisar wakilan tarayya mai wakiltar Owerri Municipal/Owerri North/Owerri West karkashin inuwar jam'iyyar PDP, kamar yadda Dailypost ta rahoto.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Meyasa suka zabi komawa inuwar APC?

Fitattun mambobin majalisar sun tabbatar da shiga APC a hukumance a wurin taron da aka shirya na musamman a filin Ndubuisi Kanu Square, Owerri, babban birnin Imo ranar Talata.

Sun bayyana cewa nagarta da kwarewar shugabancii da nasarorin da gwamna Hope Uzodinma ya samu a shekaru uku da rabi da suka gabata ne suka ja hankalinsu zuwa APC.

Legit.ng Hausa ta fahimci cewa magoya bayan 'yan majalisun uku sun jawo wasu mambobin sauran jam'iyyun siyasa a jihar Imo.

Kun yi abinda ya dace - APC

A jawabin maraba, shugaban APC na jiha, Macdonald Ebere, ya ce matakin da suka ɗauka na shiga jam'iyyar mai mulki, "Shi ne mafi a'ala a gare su."

Kara karanta wannan

Zaben Majalisa: An Gano Wanda Tsofaffin ‘Yan Majalisar Tarayya Suke Goyon Baya a APC

Bugu da ƙari, 'yan majalisun sun sha alwashin goyon bayan gwamna Uzodinma, wanda ke kokarin tazarce kan kujerarsa a zaben gwamna mai zuwa ranar 11 ga watan Nuwamba, 2023.

A wani labarin kuma Zulum Da Buni Ke Kan Gaba a Tseren Zama Shugaban Kungiyar Gwamnoni NGF

Gwamna Babagana Zulum na cikin gwamnonin APC da ka iya zama shugaban kungiyar gwamnoni Najeriya (NGF).

Ana ganin gwamnoni 2 na arewa ke sahun gaba a ɗarewa mukamin a zangon mulki na gaba.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262