Babu Murdiya, Babu Magudi – Minista Ya Ambaci Silar Nasar Tinubu a Zaben 2023

Babu Murdiya, Babu Magudi – Minista Ya Ambaci Silar Nasar Tinubu a Zaben 2023

  • Raji Babatunde Fashola ya hakikance a kan jam’iyyar APC ta ci zaben 2023 ba tare da magudi ba
  • Ministan ayyuka da harkokin gidajen kasar nan ya nuna ba a banza Bola Tinubu ya yi nasara ba
  • Fashola ya ce APC ta dade tana shiryawa zaben Shugaban kasa, hakan ya jawo aka doke PDP da LP

Abuja - Raji Babatunde Fashola SAN bai yarda cewa murdiya da magudin zabe ya yi sanadiyyar lashe zaben Asiwaju Bola Ahmed Tinubu a 2023 ba.

Da The Nation ta yi hira da Ministan ayyuka da harkokin gidajen tarayyar, ya yi bayanin irin matakan da jam’iyyar APC ta bi wajen samun galaba.

Babatunde Fashola wanda shi ne Darektan tsare-tsaren zabe da sa ido na APC a 2023, ya ce dogon tanadin da akayi, shi ya ba ‘dan takaransu sa’a a bana.

Kara karanta wannan

Shawarar da Gwamnoni Suka Ba Tinubu Tana Neman Jawo Yaki a Majalisar Tarayya

Atiku Abubakar da Peter Obi da suka nemi shugabancin Najeriya su na kotu bisa zargin APC ta yi magudi, amma Ministan ya ce magudi bai yi aiki ba.

APC ta rika bibiyar sakamakon zabe

A hirar da aka yi da shi, an rahoto Ministan yana kalubalantar abokan adawa da su nuna yadda suka shiryawa zaben, yake cewa APC ta fi kowa kintsawa.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Fashola yake cewa babu wata jam’iyya da ta ke da dakin tattarawa da kula da sakamakon zabe kamar yadda APC tayi a zabukan 2015, 2019 da na 2023.

Bola Tinubu
Dawowar Bola Tinubu daga Faransa Hoto: @BuhariSallauOnline
Asali: Facebook

A 2019, tsohon Gwamnan Legas ya ce shi ya jagoranci dakunan, haka aka maimaita a bana.

Jagoran na jam’iyya mai-ci yake cewa sun samu matasa masu jini a jiki da suka rika amfani da alkaluma, taswirori tare da shiryawa wakilan jam'iyya horo.

Kara karanta wannan

Saura Kwana 40 a rantsar da Tinubu, Buhari Ya Amince A Gina Titunan Naira Tiriliyan 1.5

"Bari in ce mun yi shiri sosai ta ciki da bai. Daga cikin shirye-shiryen shi ne horas da wakilai 2000. Su aka tura domin horas da sauran wakilai.
Wannan wani bangare kurum kenan, mun nuna masu bambancin dokar zaben 2010 da abin da za su gani a 2023, su suka zama wakilan ‘yan takara."

- Babatunde Fashola

Darektan yakin zaben shugaban kasar ya ce ba su dauki abin da wasa ba, sun yi aiki da Fuad Oki wanda ya yi suna wajen harkar kamfe a kasar Amurka.

Sai Tinubu ya yi hattara - Danbilki

A rahoton da aka fitar a ranar Litinin, an ji Abdulmajid Danbilki Kwamanda ya ce ana kokarin dawo da Rabiu Kwankwaso cikin Jam’iyyar APC mai mulki.

‘Dan siyasar ya nuna a matsayinsu na ‘yan APC a Arewa, ba za su yarda da wannan yunkuri ba domin su na ganin Kwankwaso bai cancanci wuri ba.

Kara karanta wannan

Zaben Adamawa: Zababben Shugaban kasa, Tinubu ya yi kira ga ‘Yan Sanda da Binani

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng