Mulkin Najeriya: Ina Karfi a Jikina Kuma a Shirye Nake, Bola Tinubu
- Zababben shugaban Najeriya, Asiwaju Bola Ahmed Tinubu, ya dawo Najeriya bayan shafe kusan wata 1 a turai
- Tsohon gwamnan jihar Legas ya yi fatali da jita-jitar yana fama da rashin lafiya, ya ce da kwarinsa kuma ya shirya tsaf
- Tinubu ya kuma bayyana farin cikinsa da dawowa gida kana ya gode wa masoya da masu fatan Alheri
Abuja - Shugaban ƙasa mai jiran gado, Asiwaju Bola Ahmed Tinubu, ya ce ya shirya ɗaukar nauyin da ya rataya kan kujera lamba ɗaya a Najeriya.
Rahoton jaridar Daily Trust ya ce Bola Tinubu ya faɗi haka ne jim kaɗan bayan ya dawo gida Najeriya daga tafiyar da ya kwashe kusan wata ɗaya a ƙasar Faransa.
Yayin da yake ƙasar waje, wasu rahotanni sun yi ikirarin cewa Tinubu ya na karkashin kulawar Likitoci kan wata cuta da ba'a bayyana ba.
Amma da yake jawabi ga dandazon magoya bayansa, waɗanda suka cika bangaren shugaban kasa a filin jirgin saman Nnamdi Azikwe, Abuja, ya ƙaryata rahoton cewa ba shi da lafiya.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
"Na ji daɗi yau dai gani na dawo, na samu cikakken hutu kuma na sarara, gajiya ta bi jiki kuma na shirya aikin da ke gabana."
"Ku manta da duk wata ƙarya da masu jin daɗin yaɗa jita-jita zasu faɗa muku, da ƙwarina, ina da ƙarfi a jikina."
- Bola Tinubu.
Yayin da aka tambayeshi kan shirinsa ga ƙasar nan, Tinubu ya ce yana kan neman shawari da shirye-shirye masu karfi da nufin haɗa tawaga mai kwari domin baiwa mara ɗa kunya da zaran ya shiga Ofis a watan Mayu.
Bayan haka ne Bola Tinubu ya wallafa Hotunan dawowarsa a shafin Tuwita, inda ya bayyana cewa yana cikin farin ciki da ya dawo gida Najeriya.
"Na yi matuƙar farin ciki da dawowa na gida kuma na yaba da yadda aka tarbe ni lokacin da na iso Abuja. Nagode da kauna da goyon bayan da kuke nuna mun."
Duk wanda na ɓata wa rai ya yi hakuri - Ishaku
A wani labarin kuma Gwamnan Taraba Ya Yi Koyi Da Buhari, Ya Roki Yan Najeriya Su Yafe Masa
Gwamna Darius Ishaku na jihar Taraba da ke arewa maso gabashin Najeriya ya roki al'ummar jiharsa su yafe masa idan wani abu ya ɓata musu rai tsawon shekaru 8.
Gwamnan ya duƙa har ƙasa a wurin taron Addu'o'i, kana ya yi wa mutane nasiha kan muhimmancin yafiya da ƙaunar juna.
Asali: Legit.ng