Gwamnan Taraba Ya Yi Koyi Da Buhari, Ya Roki Yan Najeriya Su Yafe Masa

Gwamnan Taraba Ya Yi Koyi Da Buhari, Ya Roki Yan Najeriya Su Yafe Masa

  • Gwamnan jihar Taraba ya nemi talakawan jiharsa da ke arewa maso gabas su yafe masa kura-kuran da ya yi
  • Darisu Ishaku, ya ce zata iya yuwuwa a lokacin mulkinsa ya ɓata wa wani, yana sane ko bai sani ba, yana neman su yafe masa
  • A makonnin da suka shige, shugaba Muhammadu Buhari da gwamna Ganduje sun nemi afuwar yan Najeriya

Taraba - Gwamna Darius Ishaku ya roki 'yan Najeriya mazauna jihar Taraba, waɗanda ya yi wa ba daidai ba a zamanin mulkinsa na tsawon shekaru Takwas, su yafe masa.

Ishaku ya nemi afuwa ne a wurin taron Addu'o'i wanda ƙungiyar Ƙiristoci (CAN) reshen jihar Taraba ta shirya masa a Sakatariyar CAN da ke Jalingo.

Gwamna Darius Ishaku.
Gwamnan jihar Taraba mai barin gado, Darius Ishaku Hoto: dailytrust
Asali: Twitter

Gwamnan ya ce ya yi farin cikin ganin yadda takensa, "Ku aminta da ni, zam kawo muku ci gaba," ya ginu ya kafa jojiyoyi a zuƙatan mutanen jihar Taraba.

Kara karanta wannan

Kano: Gwamna Ganduje Ya Roki Alfarma Ɗaya Tal Daga Wurin Zababɓen Gwamna Abba Gida-Gida

Daily Trust ta rahoto gwamna Ishaku na rokon mazauna Taraba su aminta tubalin zaman lafiya, soyayya da yafiya su jagoranci mu'amalarsu da sauran abokan zamansu.

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

Ishaku ya duƙa kan guiwowinsa yana neman afuwar talakawa

Haka nan tun kafin wannan, a wurin taron addu"o'in godiya na musamman lokacin bikin Ista a Cocin Anglican da ke Mayo Dasa, Gwamna Ishaku ya duƙa kan guyawunsa ya baiwa talakawa haƙuri.

Gwamnan ya duƙa har ƙasa a gaban dandazon taron Jama'a ya nemi su yafe masa kura-kuran da ya yi musu a lokacin zangon mulkinsa na tsawon shekaru 8.

Darius Ishaku ya ce:

"A matsayin shugaba wanda ya jagoranci jiha na tsawon shekara Takwas, mai yuwuwa na ɓata wa wasu rai ina sane ko kuma ban sani ba yayin kokarin sauke nauyin da aka ɗora mun a matsayin zaɓaɓɓen gwamna."

Kara karanta wannan

Yanzu-Yanzu: Kwamishinan Zaben Jihar Adamawa Ya Ɓace Ɓat, INEC Ta Faɗi Gaskiya

Ishaku ya ƙara da cewa littafin bayibul ya koyar da cewa mutum ya fito fili ya ba da haƙuri kana ya nemi yafiyar waɗanda ya ɓata wa rai.

"Bibble ya koya mana mu yafe wa waɗanda suka mana ba daidai ba, saboda haka ina rokon waɗanda na yi wa laifi su yafe mun. Na nemi yafiya a ɗakin Allah, duk wanda bai haƙura ba ya rage tsakaninsa da Allah."

Legit.ng ta tattaro cewa a makon da ya gabata, shugaban ƙasa, Muhammadu Buhari, ya roki 'yan Najeriya, waɗanda mai yuwuwa ya ɓata musu rai su yi haƙuri su yafe masa.

Mako ɗaya gabanin haka, gwamna Abdullahi Umar Ganduje, ya nemi afuwar mutanen jihar Kano, kamar yadda jaridar Punch ta ruwaito.

Ganduje ya nemi alfarma a wurin Abba Gida-Gida

A wani labarin kuma Gwamna Ganduje ya aike da muhimmiyar buƙata ɗaya ga sabon gwamna mai jiran gado a jihar Kano.

Kara karanta wannan

Abin Al'ajabi a Najeriya: Wani Bawan Allah Ya Sha Mamakin Kuɗin Da Ya Samu Bayan Ya Roki Allah $100m

A sakon barka da sallah, gwamna Ganduje ya yi bayanin muhimmancin ƙarisa ayyukan raya ƙasa ba tare da nuna banbancin siyasa ba don ci gaban al'umma.

Jam'iyyar APC ta yi rashin nasara a zaɓen gwamnan jihar Kano da aka gudanar ranar 18 ga watan Maris, 2023.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262