Cikakken Jerin Sunayen 'Yan Takarar PDP, APC Da Labour Party a Zaben Gwamnan Jihar Kogi

Cikakken Jerin Sunayen 'Yan Takarar PDP, APC Da Labour Party a Zaben Gwamnan Jihar Kogi

Jihar Kogi wacce ke a yankin Arewa ta tsakiya na shirin zaɓen sabon gwamna, sannan jam'iyyu da dama sun fara zaɓen ƴan takarar da za su wakilce su a zaɓen wanda zai gudana a ranar 11 ga watan Nuwamban 2023.

Jihar Kogi na ɗaya daga cikin jihohi uku waɗanda za ayi zaɓen gwamnonin su nan gaba a cikin wannan shekarar.

Waɗannan zaɓukan sun yi daban da manyan zaɓukan 2023 saboda hukunce-hukuncen kotu da suka faru a wancan zaɓen da ya gabata a jihohin.

Yan takarar gwamnan jihar Kogi
'Yan Takarar PDP, APC Da Labour Party a Zaben Gwamnan Jihar Kogi Hoto: Senator Dino Melaye, Ahmed Usman Ododo, Adejo Okeme
Asali: Facebook

Sanata Dino Melaye ya zama ɗan takarar jam'iyyar Peoples Democratic Party (PDP), Ahmed Usman-Ododo zai wakilci jam'iyya mai mulki All Progressives Congress (APC), yayin da Adejo Okeme ya samu tikitin jam'iyyar Labour Party (LP)

Manyan ƴan takarar gwamnan jihar Kogi

Sanata Dino Melaye - ɗan takarar PDP

Kara karanta wannan

Jerin 'Yan Takarar Gwamna Na APC, PDP da LP a Zaben Gwamna a Watan Nuwamba, 2023

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

Dan takarar PDP a zaben gwamnan Kogi
Sanata Dino Melaye, dan takarar gwamnan PDP a zaben jihar Kogi Hoto: Dino Melaye
Asali: Facebook

Sanata Dino Melaye tsohon sanatan Kogi ta Yamma ya samu nasarar lashe tikitin takarar gwamna a ƙarƙashin inuwar jam'iyyar PDP, na zaɓen jihar Kogi wanda za a yi a ranar 11 ga watan Nuwamban 2023.

Dino ya samu ƙuri'u 313 inda yayi nasara akan Jabiru Usman wanda ya samu ƙuri'u 127 a zaɓen fidda gwani.

Ahmed Usman Ododo - ɗan takarar APC

Dan takarar APC a zaben gwamnan Kogi
Ahmed Usman Ododo, dan takarar APC a zaben gwamnan jihar Kogi Hoto: Usman-Ododo
Asali: Facebook

Ahmed Usman-Ododo ya lallasa Shaibu Audu, Stephen Ochen, Sanusi Ohiare, Smart Adeyemi a zaɓen fidda gwani na jam'iyyar APC.

Jam'iyyar ta zaɓi ta yi zaɓen fidda gwani na ƙato bayan ƙato inda Usman-Ododo ya samu ƙuri'u 78,704, Audu ya samu ƙuri'u 763, Ochen ya samu ƙuri'u 552, Ohiare ya samu ƙuri'u 424, sannan Adeyemi ya samu ƙuri'u 31.

Usman-Ododo shine ɗan takarar da gwamnan jihar Yahaya Bello ya ke marawa baya.

Kara karanta wannan

Fintiri Vs Binani: INEC Ta Baiwa Wanda Ya Lashe Zaben Gwamnan Adamawa Shaidar Samun Nasara

Adejo Okeme - ɗan takarar Labour Party

Dan takarar LP a zaben gwamnan jihar Kogi
Barr. Adejo Okeme, dan takarar gwamnan jihar Kogi a Labour Party Hoto: Adejo Okeme
Asali: Facebook

Barr. Adejo Okeme ya lallasa mai bi masa Isaac Alfa a zaɓen fidda gwanin gwamnan jihar na jam'iyyar Labour Party (LP)

Ɗan takarar gwamnan na jam'iyyar LP ya samu ƙuri'u 127, yayin da Alfa ya samu ƙuri'u 69 a zaɓen fidda gwanin.

Okeme lauya ne kuma ɗan kasuwa wanda ya fito daga yankin mazaɓar sanatan Kogi ta Gabas.

Gwamna Zulum: Na Ji Daɗi Kasancewa Tinubu Da Shettima Ne Za Su Gaji Buhari

A wani rahoton na daban kuma, gwamnan jihar Borno, Farfesa Babagana Umara Zulum, ya farin cikin sa kan kasancewa Tinubu da Shettima a matsayin waɗanda za su mulki ƙasar nan.

Gwamnan ya ce hankalin sa ya kwanta sanin cewa ƙasar nan ta samu magadan shugaba Buhari, waɗanda suka cancanta.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng