Zaben Majalisa: An Gano Wanda Tsofaffin ‘Yan Majalisar Tarayya Suke Goyon Baya a APC

Zaben Majalisa: An Gano Wanda Tsofaffin ‘Yan Majalisar Tarayya Suke Goyon Baya a APC

  • Wasu tsofaffin ‘yan majalisar wakilan tarayya sun nuna za su marawa Muktar Betara Aliyu baya
  • Duk da ba su majalisa a yanzu, ‘yan siyasar za su iya amfani da tasirinsu a zaben da za ayi a bana
  • Hon. Betara yana cikin ‘Yan majalisar APC da ke hangen kujerar Rt. Hon. Femi Gbajabiamila

Abuja - Kungiyar tsofaffin ‘yan majalisar wakilan tarayya daga bangarori shida na kasar nan, su na tare da Hon. Muktar Betara Aliyu a zaben bana.

Rahoton Daily Trust na Litinin ya nuna tsofaffin ‘yan siyasar su na ganin ‘dan majalisar na Biu/Bayo/Shani/Kwaya Kusar ya dace da rike majalisa.

Wadannan mutane da suka wakilci mazabunsu a jam’iyyu dabam-dabam daga 2007, 2011, 2015 har zuwa 2019 sun yaba da cancantar Muktar Betara Aliyu.

Tsofaffin ‘yan majalisar da suka yi na’am da takarar Betara sun hada da Emeka Anohu, Golu Timothy, Hon. Segun Odebumi da Hon Nado Karibo.

Kara karanta wannan

Shawarar da Gwamnoni Suka Ba Tinubu Tana Neman Jawo Yaki a Majalisar Tarayya

Babale, Almakura sun yi na'am

Hon. Bashir Babale da Hon. Mohammed Almakura duk sun nuna goyon bayansu ga Betara domin ya canji Femi Gbajabiamila a majalisar tarayyar kasar.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

A karshen zaman da suka yi, Tribune ta ce tsofaffin abokan aikin ‘dan majalisar na Borno sun ce Najeriya ta na bukatar wanda zai iya hada-kan Najeriya.

‘Yan Majalisar Tarayya
Shugaban Majalisar Tarayya Hoto: @SpeakerGbaja
Asali: Twitter

Zuwa yanzu ba a san matsayar da jam’iyya mai ci ta dauka a game da zaben shugabannin majalisa ba.

Wase, Betara da Jaji ne a gaba

Wani rahoto da aka fitar a Vanguard, ya nuna takarar da ake yi ta koma tsakanin Aliyu Betara, Ahmed Wase, da Aminu Sani Jaji, dukkansu daga Arewa.

Akwai wasu ‘yan takaran kamar Abdulraheem Olawuyi, Abubakar Yalleman, Alhassan Doguwa, Abubakar Yalleman, Tajudeen Abbas da Miriam Onuoha.

Sai dai alamu na nuna wadancan mutane uku da suka fito daga Borno, Filato da Sokoto sun fi karfi.

Kara karanta wannan

‘Yan Adawa Sun Fito Gaba da Gaba Domin Karbe Shugabancin Majalisa a Hannun APC

Duk da haka, wasu za su ga Betara ya fito daga yanki guda da Kashim Shettima, amma akwai masu ganin a haka Yarbawa suka samu kujerar a 2019.

NNPP ta samu rinjaye a Kano

A wani rahoto da muka kawo, an samu bayanin adadin 'Yan majalisar dokokin da Jam’iyyar NNPP ta tsira da su a Kano bayan kammala zaben bana.

Jam’iyyar adawa ta PDP ba ta tsira da ko da cokali a duka zabukan da aka yi a 2023 ba. NNPP mai alamar kayan dadi ta na da kujeru 24, APC kuma 16.

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng

iiq_pixel