Jagoran APC Ya Zargi Tinubu da Zawarcin Kwankwaso, Ya Ja Masa Kunne Tun da Wuri

Jagoran APC Ya Zargi Tinubu da Zawarcin Kwankwaso, Ya Ja Masa Kunne Tun da Wuri

  • Abdulmajid Danbilki Kwamanda ya ce na kokarin dawo da Rabiu Kwankwaso cikin Jam’iyyar APC
  • ‘Dan siyasar ya nuna a matsayinsu na ‘Ya ‘yan APC a Arewa, ba za su yarda da wannan yunkuri ba
  • Danbilki Kwamanda ya na ganin Kwankwaso bai cancanci wuri ba domin bai taimakawa Tinubu ba

Kano - Fitaccen ‘dan siyasar nan kuma daya daga cikin jagorori a APC, Abdulmajid Danbilki Kwamanda, ya yi wani kira ga Asiwaju Bola Ahmed Tinubu.

Leadership ta ce Alhaji Abdulmajid wanda aka fi sani da Danbilki Kwamanda, yana so zababben shugaban kasar ya ajiye batun zawarcin Rabi’u Musa Kwankwaso.

‘Dan siyasar yana zargin Bola Ahmed Tinubu yana kokarin maido da Rabi’u Musa Kwankwaso cikin jam’iyyar APC, yace hakan ba zai taimaki jam’iyyarsu ba.

Danbilki Kwamanda ya yi wannan bayani da ya zanta da manema labarai jiya a garin Kano.

Kara karanta wannan

Shawarar da Gwamnoni Suka Ba Tinubu Tana Neman Jawo Yaki a Majalisar Tarayya

Kwamanda ya ce hakan hadari ne

A cewar Kwamanda, sun gano zama da za ayi a asirce tsakanin shugaba mai jiran gado da kuma tsohon Gwamnan Kano da ya yi takarar shugaban kasa a NNPP.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Idan aka yi nasarar karkato da hankalin Rabiu Kwankwaso har ya sauya-sheka, hakan zai yi wa jam’iyyar APC illa a matakin jiha da kasa, a cewar ‘dan siyasar.

Kwankwaso
Tinubu, Akande da Kwankwaso a 2014 Hoto: pmnewsnigeria.com
Asali: UGC

Baya ga jefa jam’iyya mai mulki da za ayi a rigingimu, Vanguard ta rahoto Danbilki Kwamanda yana mai hakan zai jawo a rasa shugabannin da ke rike da APC.

“Bola Tinubu yana zawarcin Rabiu Kwankwaso a boye. Watakila yana yi masa kallon shahararre, shiyasa yake son ya hade da shi.
A Arewa, mu ba za mu yarda a hada-kai da Kwankwaso ba. Za mu yaki lamarin da karfinmu. Kwankwaso bai taimaki Tinubu ya ci zabe ba.

Kara karanta wannan

Barka da Sallah: Atiku Ya Fadi Abin da Yake Damunsa, Tinubu Ya Yi kira ga Musulmi

Ba za mu yarda Tinubu ya hada-kai da Kwankwaso saboda ya sauya sheka zuwa jam’iyyar APC ba.
Idan hakan ta tabbata, za mu yaki Tinubu da APC a Arewa. Ba mu gamsu da siyasar Kwankwaso ba, mu na jan kunnen Tinubu a kan jawo shi.”

- Abdulmajid Danbilki Kwamanda

Zaben Shugabannin majalisa

Ba a nan Kwamanda ya tsaya bam ya bukaci shugabannin jam’iyyar APC na kasa da su ware kujerar shugaban majalisar dattawa zuwa ga Arewa maso yamma.

Yin hakan zai ba gwanin Danbilki watau Sanata Barau Jibrin damar zama shugaban majalisa.

Wani rahoton ya ce ce shahararren ‘dan siyasar na Kano ya tallata Sanata mai wakiltar Arewacin jihar yayin da ya zanta da manema labarai a sakatariyar NUJ.

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng