Wasu Kungiyoyi Sun Bayyana Shiyyar da Ya Dace Ta Fitar da Shugaban Majalisar Dattawa
- Kungiyoyi sun bayyana shiyyar da ya kamata jam'iyyar APC ta baiwa kujerar shugaban majalisar dattawa ta 10
- Kodinetan ƙungiyoyin ya nemu shugabanni APC su goyi bayan Sanata Barau Jibrin, daga jihar Kano saboda wasu dalilai
- Tun bayan kammala zabe, aka fara fafutukar neman muƙamai a majalisar tarayya ta 10 da za'a rantsar nan gaba
Gamayyar ƙungiyoyin da ke sha'awar tsoma baƙi a harkokin siyasa a arewa maso yamma, 'Rescue North West APC Group' ta ce ta raba gardama kan kujerar shugaban majalisar dattawa.
Punch ta rahoto gamayyar ƙungiyoyin na cewa shiyyar arewa maso yammacin Najeriya ce ta cancanta ta samu kujerar shugaban majalisar dattawa ta 10 da za'a kafa.
A cewarsu, ya kamata a baiwa shiyyar wannan kujera saboda ta ba da gudummuwar tulin ƙuri'u, waɗanda suka taimaki zababben shugaban ƙasa, Bola Tinubu, ya kai ga nasara a zaɓen 2023.
Wane Sanata ya dace da muƙamin shugaban majalisar dattawa?
Bayan taron da ƙungiyoyin suka gudanar a jihohin Katsina, Kaduna, Kano, Jigawa, Kebbi da Sakkwato, sun cimma matsayar goyon bayan Sanata Barau Jibrin.
DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar
Wannam matsaya na ƙunshe a wata sanarwa da Kodinetan gamayyar ƙungiyoyin, Muktar Dahiru-Gore, ya rabawa manema labarai ranar Laraba.
Wani sashin sanarwan ya ce:
"Arewa ta yamma ta ba da gagarumar gudummuwar ƙuri'u da suka taimaka wa jajirtaccen shugaban kasar mu mai jiran gado, Asiwaju Bola Tinubu, ya lashe babban zaɓen 2023."
"Shiyyar ce ta baiwa jam'iyyar APC kaso 30 cikin 100 na kuri'un da suka ɗaga zababben shugaban ƙasa ya ci zaɓe."
"Saboda haka muna kira ga kwamitin gudanarwa da shugaban APC, Abdullahi Adamu, da sauran masu kishi, a baiwa arewa maso yamma kujerar shugaban majalisar dattawa."
"Haka nan bayan miƙa wa shiyyar kujerar, a baiwa Sanata Barau Jibrin, wada ya fi sauran gogewar aiki daga shiyyar arewa maso yamma. Ya koma Sanata karo na uku kenan."
Buhari ya maida wa Ortom martani mai zafi
A wani labarin kuma Shugaba Buhari Ya Tona Asirin Wani Gwamnan Arewa Wanda Ya Sha Kaye a Zaɓen 2023
Shugaba Muhammadu Buhari ya ce ba bu ta yadda talakawa zasu ƙara aminta da gwamna Samuel Ortom a jihar Benuwai saboda ba abinda ya yi musu a shekara 8.
A wata sanarwa da Mallam Garba Shehu ya fitar, Buhari ya ce gwamna Ortom ke hana gwamnatin tarayya kai ɗauki don magance matsalar tsaro a jiharsa.
Asali: Legit.ng