Bola Tinubu Ya Bukaci Yan Sanda Su Binciki Rudanin Zaben Adamawa
- Bola Tinubu, zababben shugaban kasa ya bukaci hukumar yan sanda ta yi bincike kan abinda ya faru a zaɓen jihar Adamawa
- Tinubu ya taya baki ɗaya wadanda suka lashe zaɓe murna bayan karisa babban zaɓen 2023 ranar 15 ga watan Afrilu
- Bayan haka Tinubu ya shawarci waɗanda zabe bai musu suga ba su bi matakan doka wajen neman haƙƙinsu
Abuja - Shugaban ƙasa ma jiran gado, Asiwaju Bola Ahmed Tinubu, ya roki rundunar 'yan sanda ta gudanar da sahihin bincike kan ruɗanin da aka samu a cikon zaɓen Adamawa.
Rahoton Vanguard ya ce Tinubu ya shawarci sauran 'yan takara da sakamakon zaɓen gwamnan Adamawa bai wa daɗi ba, su bi hanyar da doka ta tanada wajen nuna adawarsu.
Tinubu ya yi wannan zancen ne a wata sanarwa da ya fitar ranar Laraba kan babban zaɓen da aka kammla a Najeriya, wanda ya rattaɓa wa hannu da kansa.
Tsohon gwamnan jihar Legas ɗin ya taya murna ga baki ɗaya waɗanda suka samu nasara a cikon zaɓen jihohin Kebbi da Adamawa wanda aka gudanar ranar 15 ga watan Afrilu, 2023.
DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka
A kalamansa, Sanata Bola Tinubu ya ce:
"Haka nam ina taya murna ga waɗanda suka samu nasarar zuwa majalisar dattawa, majalisar wakilai da majalisar dokokin jihohi a yankunan da zaɓen ciko ya gudana."
"Waɗannan maza da mata da suka ci zaɓe sun samu sahalewar mutanen mazaɓarsu, saboda haka ina kira garesu da su sadaukar da kansu wajen sauke nauyin talakawa."
"Ƙarishen zaben da aka kammala ya tabbatar da babbam zaɓen 2023 ya zo ƙarshe. Na gamsu da yadda cikon zaɓen da ya gabata ranar Asabar ya gudana cikin kwanciyar hankali."
Me Tinubu ya faɗa game da zaɓen Adamawa?
Punch tace yayin da yake tsokaci kan abinda ya faru a jihar Adamawa, Tinubu ya ƙara da cewa:
"Na ga abinda ya faru a cikon zaɓen gwamnan jihar Adamawa, kuma ina rokon hukumar yan sanda ta gudanar da cikakken bincike kan abinda ya haddasa ruɗani."
"A duk wani zaɓe mutum ɗaya ne ke zama zakara, ina fatan waɗanda sakamako bai masu daɗi ba za su bi matakan doka wajen nuna fushinsu."
A wani labarin kuma Jerin Sanatocin PDP 6 Da Ka Iya Neman Shugaban Marasa Rinjaye a Majalisa Ta 10
Yayin da aka kammala babban zaɓen 2023 a Najeriya, hankali ya koma majalisar tarayya, inda ak fara fafutukar nemna manyan muƙamai.
Kamar dai yadda take wakana a jam'iyyar APC, mun haɗa muku manyan Sanatoci da ka iya zama shugaban marasa rinjaye a majalisar dattawa.
Asali: Legit.ng