Ba Jira: INEC Ta Sanya Lokacin Ba Gwamnan Adamawa Satifiket Din Lashe Zabe
- Hukumar zaɓe mai zaman kanta ta ƙasa (INEC) tace yau gwamnan Adamawa zaiɓsamu satifiket ɗin lashe zaɓe
- Hukumar tace yau Laraba da rana za ta ba gwamnan da mataimakiyarsa satifiket ɗin lashe zaɓe
- Ahmadu Umar Fintiri ya samu nasarar komawa kan kujerar sa bayan ya lallasa Aisha Binani ta APC
Jihar Adamawa - Hukumar zaɓe mai zaman kanta ta ƙasa, (INEC) ta sanar da cewa biyo bayan kammala zaɓen cike gurbi na gwamnan jihar Adamawa, a yau za ta miƙa satifiket ɗin lashe zaɓe ga gwamna Fintiri, rahoton Tribune ya tabbatar.
Idan ba a manta ba dai a ranar Talata ne hukumar INEC ta bayyana gwamnan jihar mai ci, Ahmadu Umar Fintiri, na jam'iyyar Peoples Democratic Party (PDP) a matsayin wanda ya lashe zaɓen gwamnan jihar.
Ahmadu Fintiri ya samu nasara ne bayan ya lallasa abokiyar hamayyar sa ta jam'iyyar All Progressives Congress (APC), Aisha Dahiru Binani.
Zaɓen cike gurbin na gwamnan jihar Adamawa ya zo da taƙaddama wacce har ta kai ga an dakatar da tattara sakamakon zaɓen, biyo bayan gaban kansa da kwamishinan INEC na jihar ya yi inda ya bayyana Binani matsayin wacce ta yi nasara ana tsaka da tattara sakamakon zaɓe.
Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!
A wata sanarwa da hukumar INEC ta fitar a shafin ta na Twitter, a ranar Laraba 19 ga watan Afirilun 2023, hukumar ta ce a yau Laraba da misalin ƙarfe 3 na rana za ta miƙa wa Ahmadu Fintiri da mataimakiyar sa satifiket ɗin lashe zaɓe.
Sanarwar na cewa:
"Biyo bayan kammala zaɓukan cike gurbi a faɗin ƙasar nan da bayyana waɗanda suka yi nasara, hukumar INEC za ta gabatar da satifiket ɗin lashe zaɓe ga gwamnan jihar Adamawa da zaɓaɓɓiyar mataimakiyar gwamna, yau da misalin ƙarfe 3 na rana."
Sanannen Malamin Addinin Musulunci Ya Caccaki Hudu Ari
A wani rahoton na daban kuma, kun ji yadda wani sanannen malamin addinin musulunci, ya caccaki kwamishinan INEC na jihar Adamawa, Hudu Yunusa Ari.
Hudu ya yi gaban kan sa inda ya bayyana wacce ta lashw zaɓe ana tsaka da tattara sakamakon zaɓen gwamnan jihar.
Asali: Legit.ng