An Zarge Shi da Bada Cin Hanci, Dino Melaye Ya Fadi Yadda Ya Samu Takarar Gwamna
- Dino Melaye ya karyata masu kukan cewa murdiya aka yi domin ya samu tikitin jam’iyyar PDP
- ‘Dan siyasar ya ce wani ‘mai’ ya rabawa masu tsaida gwani, hakan ya sa ya zama ‘dan takara
- Melaye bai iya amsa tambayar da aka yi masa a kan zargin tasirin kudi a zaben da ya yi nasara ba
Abuja - Dino Melaye wanda zai rikewa jam’iyyar PDP tuta a zaben sabon Gwamnan jihar Kogi, ya musanya zargin da ake yi masa na sayen takarara da kudi.
Da aka yi hira da shi a tashar talabijin nan na Channels a yammacin Talata, Sanata Dino Melaye ya bada amsa ga masu korafi kan zaben gwanin da ya lashe.
Ana zargin an yi magudi kafin a tsaida tsohon Sanatan a matsayin ‘dan takaran Gwamna, amma ya ce ba haka abin yake ba, Ubangiji ne ya taimake shi.
Melaye yake cewa ba komai ya jawo masu tsaida ‘dan takaran suka zabe shi ba sai wani mai da ya raba masu, ya ce wannan man albarkan ya yi masa aiki.
Zaben tsaida gwani ya bar baya da kura
Rahotanni sun zo cewa wanda ya zo na biyu a zaben fitar da gwanin da Ahmad Muhammad Makarfi ya shirya shi ne Jabiru Usman mai kuri’u 127.
DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar
Tsohon Mataimakin Gwamna, Yomi Awoniyi yana da kuri’u 77 sai Musa Wada ya samu 56. Tribune ta fitar da rahoton hirar da aka yi da 'dan takaran.
A zaben da ya samu kuri’u 313, wasu daga cikin abokan takararsa sun yi korafin an canza masu zabe, Dino ya fadawa tashar cewa hakan ba gaskiya ba ne.
Yomi Awoniyi ya zargi Sanata Abdul Ningi da hada-kai da Dino wajen canza masu fitar da ‘dan takara, a dalilin haka ya ce sam bai yarda da sakamakon ba.
Mahaifiyar Wani Dan Najeriya Da Ke Kasar Waje Ta Bar Shi Da Cizon Yatsa Bayan Cinye Kudin Da Ya Ke Aiko Mata
Cin hanci: A tambayi EFCC, ICPC
Da aka tambaye shi ko kudi ya yi tasiri a zaben shi, tsohon Sanatan na Kogi ta yamma ya ce jami’an ICPC da EFCC za su fi shi sanin ko an bada cin hanci.
"Ni ba ma’aikacin EFCC ko ICPC ba ne. Ba zan san ko an raba kudi ba.
Amma idan a matsayina ba zan iya daukar dawainiyar zaben tsaida gwanina ba, akwai matsala a wani wurin."
- Dino Melaye
A cewarsa, Ubangiji ne ya tallafa masa, yana mai tsakuro wata aya daga cikin surar Philippians a littafin Injila, yana mai nuna falalar Yesu Almasihu ya samu.
Ba da Binani nayi takara ba - Fintiri
Gwamna Ahmadu Umaru Fintiri ya fito yana cewa bai yi takara da wata mace a jihar Adamawa, an rahoto shi ya ce ya yi takara da makiyan damukaradiyya ne.
Kamar yadda Ahmadu Umaru Fintiri ya fada da aka zanta da shi, taron dangi aka yi masa, masu jin su ne suka mallaki Najeriya sun dage sai sun hana shi tazarce.
Asali: Legit.ng