Daga Karshe Ranar Da INEC Za Ta Bayyana Sakamakon Zaben Gwamnan Jihar Adamawa Ta Bayyana

Daga Karshe Ranar Da INEC Za Ta Bayyana Sakamakon Zaben Gwamnan Jihar Adamawa Ta Bayyana

  • Akwai yiwuwar hukumar zaɓe mai zaman kanta ta ƙasa (INEC) ta bayyana wanda ya lashe zaɓen gwamnan Adamawa cikin satin nan
  • Hukumar za ta yi zama a hukumance domin samar da matsaya kan zaɓen gwamnan jihar ta Adamawa
  • Zaɓen gwamnan jihar Adamawa ya kasance mai cike da ruɗani biyo bayan taƙaddamar da ya janyo

Abuja - Idan dai har wani sauyin da ba ayi tunani samun sa aka samu ba, hukumar zaɓe mai zaman kanta ta ƙasa (INEC) za ta sanar da sakamakon gwamnan jihar Adamawa a ranar Alhamis, a cewar jaridar Vanguard.

Kwamishinan INEC na ƙasa, Festus Okoye, ya bayyana cewa INEC za ta yi taro a hukumance a tsakanin ranar Talata da Laraba kan lamarin.

Ranar Alhamis INEC za ta bayyana sakamakon zaben gwamnan Adamawa
Gwamnan jihar Adamawa, Ahmadu Fintiri da Aisha Dahiru Binani Hoto: Channels tv
Asali: Twitter

Daily Trust tace a ranar Litinin hukumar INEC ta dakatar da kwamishinan ta na jihar Adamawa, Mr. Hudu Yunusa-Ari, bisa kwace ƙarfin ikon baturen zaɓen jihar inda yayi gaban kansa ya bayyana Aisha Binani ta jam'iyyar APC, matsayin wacce ta lasbe zaɓen gwamnan jihar.

Kara karanta wannan

Wani Gwamna Ya Dira Yola, Ya Yi Kus-Kus da Fintiri Kan Ayyana Binani a Matsayin Gwamnan Adamawa

Da aka tambaye shi ko yaushe za a ci gaba da tattara sakamakon zaɓen, sai Okoye ya kada baki ya ce, sai INEC ta fara zama a hukumance domin sanya ranar da za a cigaba da tattara sakamakon zaɓen.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Taron a hukumance yana nufin zama tsakanin shugaban hukumar na ƙasa da kwamishinoni 12 na ƙasa na hukumar.

A cewar Okoye, da yawa daga cikin kwamishinonin hukumar na ƙasa, an tura su wasu jihohi domin sanya ido kan zaɓukan cike gurbin da aka yi ƙarshen satin da ya wuce, inda ya ce mafi yawa daga cikin su suna kan hanyar komawa birnin tarayya Abuja.

A kalamansa:

"Sai hukumar INEC ta zauna a hukumance domin yanke hukunci kan ci gaba da tattara sakamakon zaɓen. Da yawa daga cikin kwamishinonin hukumar na ƙasa an tura su jihohi daban-daban. An tura ɗaya jihar Kebbi, wani jihar Oyo, wani jihar Sokoto da sauran su."

Kara karanta wannan

Jam'iyyar APC Ta Doke Manyan Abokan Karawarta, Ta Lashe Ƙarin Kujerun Yan Majalisa 8

"Suna kan hanyar dawowa Abuja. Idan sun iso Abuja a daren ranar Litinin, akwai yiwuwar hukumar ta zauna ranar Talata domin yanke shawara kan ranar ci gaba da tattara sakamakon zaɓen."

Sai dai majiyoyi a hukumar sun bayyana cewa hukumar zaɓen ba ta son ƙara jan ƙafa kan lamarin, idan dai har ba doka ba ce ta sa hakan, inda aka ƙara da cewa za a cigaba da tattara sakamakon zaɓen kafin wannan satin ya ƙare domin kwantar da hankulan da suka tashi a. jihar.

Jam'iyyar PDP Ta Shiga Zanga-Zanga a Adamawa, Ta Sha Wani Muhimmin Alwashi

A wani rahoton na daban kuma, kun ji yadda jam'iyyar PDP a jihar Adamawa ta tsunduma cikin zanga-zanga kan sakamakon zaɓen gwamnann jihar.

Jami'iyyar ta PDP tana neman dole sai an dawo an kammala tattara sakamakon zaɓen gwamnan jihar wanda hukumar INEC ta dakatar.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng