Zaben Majalisa: Sanatan APC Ya Samu Goyon Bayan ‘Yan Majalisar Kano da Jigawa
- A zaben shekarar nan da za ayi a majalisa, Sanata Danladi Sankara ya bi bayan takarar Barau Jibrin
- Sankara bai cikin wadanda za su yi zabe a majalisa ta goma, Husaini Babangida Uba zai canji kujerarsa
- Idan ana maganar cancanta, Mas’ud El-Jibril yana ganin Jibrin ya sha gaban duk wani Sanata mai-ci
Abuja - Sanata Danladi Sankara da tsohon Sanata, Mas’ud El-Jibril sun tashi tsaye wajen ganin Barau Jibrin ya zama shugaban majalisar dattawa.
The Nation ta ce Danladi Sankara mai wakiltar Jigawa ta Arewa maso yamma majalisar dattawa da Mas’ud El-Jibril sun ga cancantar Barau Jibrin.
Sanata Barau Jibrin mai wakiltar yankin Arewacin jihar Kano yana cikin wadanda suke neman shugabancin majalisa ta koma a karkashin APC.
Ganin ya dade ana damawa da shi a majalisar tarayya, Alhaji Danladi Sankara ya ce Jibrin ya kamata ya jagoranci Sanatocin kasar a zaben bana.
Maganar Danladi Sankara
A wannan gaba, Barau Jibrin shi ne ya fi dacewa da kujerar shugaban majalisar dattawa.
DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka
Idan ya hau wannan kujerar, zai yi amfani da gogewarsa wajen bada jagoranci na kwarai ta hanyar tafiya da mutane da zai taimaki gwamnati.
- Danladi Sankara
Da sharadin sai ware kujerar zuwa Arewa
‘Dan majalisar na Jigawa ya ce muddin aka ware kujerar zuwa Arewa maso yamma, babu wani wanda ya fi Sanatan na jihar Kano ta Arewa dacewa.
A karkashin jagorancin tsohon ‘dan majalisar wakilan tarayyar, an rahoto Sanata Sankara yana cewa shugabancin Jibrin zai amfanar da ‘yan Najeriya.
Mas’ud El-Jibril ya bi Jibrin
A na shi bangaren, Mas’ud El-Jibril ya ce mutumin jihar ta sa yana da kwazo, sannan kuma abokan aikinsa su na ganin girmansa sosai a majalisar dattawa.
"Na tabbata duk mukamin da Jibrin zai rike a kasar nan, ba za a same shi da gazawa ba domin yana da gaskiya, kuma yana da abokai da masoya da-dama.
Baya ga haka, shi rikakken ‘dan siyasa ne wanda yake tare da jama’a."
- Mas’ud El-Jibril
Ana haka ne sai aka ji Kassim Afegbua da ‘yan kungiyarsa su na bada shawarar cwanda zai zama shugaban majalisar dattawa ya fito daga Kudu ta kudu.
Buhari yana Makkah
An ji labari Muhammadu Buhari ya zanta da Gwamnonin jihohin Borno da Yobe, Tukur Buratai da Abike Dabiri-Erewa a Birnin Makkah a Saudi Arabiya.
Shugaba mai barin gado ya je kasa mai tsarki domin ya yi Umrarsa ta karshe a kan karagar mulki. Nan da kwanaki 44 ne Buhari zai ba Bola Tinubu wuri.
Asali: Legit.ng