Yanzu Yanzu: Tambuwal Ya Lashe Zaben Sanata Mai Wakiltan Sokoto Ta Kudu
- Gwamna Aminu Waziri Tambuwal ya lashe zaben ciko da aka yi a yankin Sokoto ta kudu
- An ayyana gwamnan na PDP a matsayin wanda ya lashe zaben a ranar Lahadi, 16 ga watan Afrilu da tazarar 4,976 tsakaninsa da babban abokin hamayyarsa
- Tambuwal ya samu kuri’u 100,860 wajen doke dan majalisa mai ci kuma dan takarar APC, Ibrahim Danbaba Dambuwa wanda ya samu kuri’u 95,884
An ayyana gwamnan jihar Sokoto, Aminu Tambuwal a matsayin zababben sanata mai wakiltan Sokoto ta kudu a ranar Lahadi, 16 ga watan Afrilu.
Tambuwal, dan takarar jam’iyyar Peoples Democratic Party (PDP) ya lallasa sanata mai ci Danbaba Dambuwa, da tazarar kuri’u 4,976, Nigerian Tribune ta rahoto.
Tambuwal ya lashe zaben sanata mai wakiltan Sokoto ta kudu
Da yake sanar da sakamakon zaben da misalin 11:55 na safiyar Lahadi a ofishin INEC a karamar hukumar Bodinga, baturen zaben, Farfesa Abubakar Abdullahi Bagudo ya ce Tambuwal ya zama zababben sanata da kuri’u 100,860.
DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar
Ya kuma sanar da cewar dan takarar APC, Abdullahi Ibrahim Danbaba, ya samu jimilar kuri’u 95,884.
Wamakko Ya Sake Komawa Kujerarsa Ta Sanata
A wani labarin makamancin wannan, mun ji cewa tsohon gwamnan jihar Sokoto kuma dan takarar jam’iyyar APC, Sanata Aliyu Wamakko ya yi nasarar lashe zaben sanata mai wakiltan Sokoto ta Arewa.
Wamakko ya lallasa babban abokin adawarsa wanda yake mataimakin gwamnan jihar, Manir Muhammad Dan’Iya na jam’iyyar PDP da tazarar kuri’u 23,023.
Baturen zabe Ibrahim Magawata ya ce, cikon zaben ya nuna Wamakko ne ya lashe shi da kuri’u 141,468.
A wani labarin kuma, shugaban masu rinjaye a majalisar wakilai ta kasa, Alhassan Ado Doguwa ya sake yin nasarar zabe a mazabarsa ta Doguwa/Tudun Wada a jihar Kano.
Wakilin hukumar zabe ta kasa mai zaman kanta, Sani Ibrahim ne ya sanar da hakan yayin da yake karanto sakamakon cikon zaben ranar Asabar 15 ga watan Afrilu.
Kamar yadda ya bayyana, Doguwa ya samu kuri’u 41,573, inda ya lallasa abokin hamayyarsa na PDP, Yushau Salisu na NNPP da ya samu kuri’u 34,831 a zaben.
Asali: Legit.ng