Fintiri v Binani, Tambuwal, Wammako da Zaben ‘Yan Takara Masu Zafi da Ake Shiryawa a Yau
- A jihar Kano za a karasa zaben kujerun majalisar wakilan tarayya 2 da na dokoki a mazabu har 14
- Sannan akwai kujeru a Kebbi da Adamawa, a Katsina akwai karashen zaben ‘yan majalisar Jiha 3.
- Aliyu Magatakarda Wammako da Magajinsa, Gwamna Aminu Tambuwal za su san makomarsu
Jam’iyyu musamman na APC, PDP, LP da NNPP da wasunsu za su shiga zabukan da hukumar INEC za ta kammala a karshen makon nan.
Rahoton nan ya tattaro zabukan da ake ganin abubuwa za su dauki zafi tsakanin ‘yan takara:
1. Fintiri v Binani
Gwamna Umaru Fintiri ya sha gaban ‘yar takarar APC, Sanata Aishatu ‘Binani’ Dahiru a zaben Adamawa, kowa zai so ganin ya sakamakon zai kasance.
Zuwa yanzu Fintiri da jam’iyyar PDP su na da kuri’u 401,113, Binani ta na da 365, 498, ta na kuma sa ran cike wannan gibi a rumfuna 142 da za a sake yin zabe.
2. Janar v Kauran Gwandu
Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!
A jihar Kebbi kuwa, jam’iyyar APC mai mulki ce ta ke gaban PDP daga sakamakon da aka sanar a kananan hukumomi 20 a cikin 21, a yau za a kammala zabukan.
A yadda aka tsaya Nasiru Idris yana da kuri’u 388,258, ya ba abokin hamayyarsa na PDP watau Janar Aminu Bande ratar 45, 278, shi kuma yana da kuri’u 342,980.
3. Tambuwal v Danbaba
A yau ne za a karkare zaben duka kujerun majalisar dattawa da ke Sokoto. Gwamna Aminu Tambuwal yana takara da Sanata mai-ci Ibrahim Danbaba na APC.
4. Wammako vs Dan Iya
A Sokoto ta Arewa kuma, tsohon Gwamna, Sanata Aliyu Magatakarda Wammako zai goge raini da Mataimakin Gwamnan jihar Sokoto mai-ci, Mannir Dan Iya.
5. Gobir v Lamido
A Sokoto ta Gabas, Shu'aibu Gwanda Gobir yana gwabzawa da Ibrahim Lamiɗo a Gada, Goronyo, Gwadabawa, Illelah, Isa, Raɓah, Sabon Birni da Wurno
Waiwaye: Yawan Kuri'un Da APC, PDP Ke Da Shi Kafin INEC Ta Ayyana Zabukan Adamawa, Kebbi a Matsayin Wadanda Basu Kammala Ba
6. Yahaya vs Kangiwa
Za a shirya zaben Sanata a rumfuna 23 da ke shiyyar Kebbi ta Arewa. ‘Dan takaran PDP shi ne Sanata Yahaya Abdullahi, yana takara da Suleiman Kangiwa.
7. Marafa v Bilbis
Mutum 47, 227 za su kada kuri’a a Bunguɗu, Maru da Tsafe a shiyyar Zamfara ta tsakiya. Takarar tsakanin Kabiru Garba Marafa da Ikira Aliyu Bilbis ne.
8. Doguwa v Soja
A jihar Kano za a karasa zaben kujerun majalisar wakilai na shiyyar Tudun Wada/Doguwa inda Alhassan Ado Doguwa yake gaban Salisu Yushau na NNPP.
9. NNPP v LP a Fagge
Za a san wanda zai wakilci mazabar Fagge a majalisar wakilai. Jam’iyyar NNPP na da kuri’u 18, 410, LP ta na da 12, 729, APC da PDP su na da 8, 194 da 6, 546.
Sabanin 'Yan NNPP a Ogun
An samu labari Kotu ta amince a canza Lauyan da ya tsayawa NNPP a zaben Ogun a sakamakon rokon da shugaban jam'yya, Olufemi Oguntoyinbo ya yi.
Amma tsohon Shugaban NNPP, ya fito yana cewa babu mutumin da ya isa ya canza Lauyan da ya tsayawa masu domin shi ne wanda ya shigar da karar.
Asali: Legit.ng