Sokoto da Kano: Yadda Zaben Cike Gurbi Ke Gudana a Jihar Kano da Sokoto a Arewa

All posts
Key Events
Analysis
Exclusive
7 Posts
Sort by
Our live updates have concluded for the day. Catch up on everything you missed below.
Aminu Ibrahim avatar Salisu Ibrahim avatar
daga Aminu Ibrahim and Salisu Ibrahim

Sakamakon zabe a Kano ya fara fitowa

Rahotanni daga jihar Kano na nuni da cewa, sakamakon cikon zaben da aka yi ya fara fitowa daga rumfuna da yawa a jihar.

Aminu Ibrahim avatar Salisu Ibrahim avatar
daga Aminu Ibrahim and Salisu Ibrahim

Ana rabon atamfa, buhun taki da N5,000 ga masu zabe a Kano

Wata jam'iyya na bada buhun taki, atamfa da N5,000 ga duk wanda zai kada mata kuri.

Lamarin na faruwa ne a akwatin zabe mai lamba 008 a gundumar Burum-Burum a karamar hukumar Tudun Wada a Kano.

Lamarin ya faru misalin karfe 1.46 na ranar yau Asabar.

Aminu Ibrahim avatar Salisu Ibrahim avatar
daga Aminu Ibrahim and Salisu Ibrahim

An ba wa hammata iska tsakanin masu zabe da wakilan jami'iyya

An yi dambe tsakanin masu kada kuri'a da wakilan jam'iyya na akwatin zabe mai lamba 024 a gundumar Badon uku uku a karamar hukumar Wamakko ta Sokoto misalin karfe 2.15 na rana.

Hakazalika, an lura da cewa ana siyan kuri'u.

Aminu Ibrahim avatar Salisu Ibrahim avatar
daga Aminu Ibrahim and Salisu Ibrahim

'Yan daba sun farmaki rumfar zabe a Kurna Gabas, sun watsa masu kada kuri'a

An fara zabe a wata rumfa a gundumar Alasawa Kwaciri a yankin Kurna Gabas a karamar hukumar Fagge ta jihar Kano.

Sai dai, an samu tsaiko a lokacin da wasu 'yan daba suka farmaki rumfar zaben tare da watsa masu kada kuri'u.

An ga jama'a maza da mata na gudun tsira, inda 'yan daban ke jifansu da duwatsu.

Daga baya, jami'an 'yan sanda sun kawo dauki, inda suka bi 'yan daban da gudu tare da koransu a harabar rumfar zaben.

Aminu Ibrahim avatar Salisu Ibrahim avatar
daga Aminu Ibrahim and Salisu Ibrahim

Ana zabe cikin lumana a Fagge

A halin da ake ciki, ana ci gaba da kada kuri'u a Fagge A da B a mazabar tarayya ta Fagge a jihar Kano.

Aminu Ibrahim avatar Salisu Ibrahim avatar
daga Aminu Ibrahim and Salisu Ibrahim

Ana zabe lami lafiya a a Kuzarawa

Masu kada kuri'a na cigaba da yin zabe cikin lumana a akwatin zabe mai lamba (006) a Kuzarawa a karamar hukumar Gaya ta Kano.

Jami'an tsaro guda uku suna wurin don tabbatar da doka da oda.

Aminu Ibrahim avatar Salisu Ibrahim avatar
daga Aminu Ibrahim and Salisu Ibrahim

An fara zabe a karamar hukumar Gaya

An fara kada kuri'a a gundumar Kazurawa a akwatin zabe mai lamba 006 da ke karamar hukumar Gaya na jihar Kano, misalin karfe 9.54 na safe.

Jami'an tsaro sun hallara.