Muhimman Abubuwa 4 da Ya Kamata Ku Sani Game da Fintiri da Binani a Adamawa
A yau 15 ga watan Afrilu, 2023, hukumar zaɓe ta shirya karisa zaben gwamna a jihar Adamawa bayan ta ayyana cewa bai kammalu ba watau Inconclusive.
Manyan yan takara biyu ne fafatawa ta yi zafi a tsakaninsu, gwamna mai ci, Ahmadu Fintiri, na jam'iyyar PDP da kuma Sanata Aishatu Ɗahiru Binani, yar takara a inuwar APC.
Fintiri ne ke kan gaba da kuri'u 421,524, yayin da Sanata Binani ke take masa baya a kusa-kusa da kuri'u 390,275, tazarar da ke tsakaninsu ba ta wuce kuri'a 31,249 ba, kamar yadda The Cable ta tattaro.
Yayin da mazauna jihar Adamawa zasu tantance wanda zai shugabance su tsawon shekaru hudu masu zuwa, Legit.ng Hausa ta tattara muku wasu muhimman batutuwa.
Muhimman Abubuwa 4 game da gwamna Fintiri
1. Gwamna Ahmadu Fintiri na neman tazarce zango na biyu a kan kujerarsa karkashin inuwar jam'iyyar PDP.
Waiwaye: Yawan Kuri'un Da APC, PDP Ke Da Shi Kafin INEC Ta Ayyana Zabukan Adamawa, Kebbi a Matsayin Wadanda Basu Kammala Ba
Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!
2. Fintiri ya lallasa gwamna mai ci, Jibrilla Bindow na jam'iyyar APC sannan ya hau kan kujerar gwamna a babban zaɓen 2019.
3. Ya kasance tsohon ɗan majalisar jiha kuma tsohon kakakin majalisar dokokin jihar Adamawa a arewa maso gabashin Najeriya.
4. An naɗa Fintiri a matsayin gwamnan riko a shekarar 2014 biyo bayan tsige gwamna Murtala Nyako.
Gaskiya 4 game da Sanata Aishatu Binani
1. Sanata Binani ta lallasa yan takara maza Shiga cikinsu har da shugaban EFCC na farko, Nuhu Ribaɗo, gabanin ta lashe tikitin takarar gwamna a inuwar jam'iyyar APC.
2. Aishatu Binani na ɗaya daga cikin Sanatoci mata 7 da suka shiga majalisar dattawa ta 9, tana wakiltar mazaɓar Sanatan Adamawa ta tsakiya.
3. Haka nan Binani ta kasance tsohuwar mamban majalisar wakilan tarayya a mazaɓar Yola North/Yola South/Girei karƙashin inuwar PDP a majalisa ta 7.
4. Idan Binani ta lashe zaɓen gwamnan Adamawa, zata kafa tarihin zama zababbiyar gwamna mace ta farko a tarihin Najeriya.
A wani labarin kuma Gwamnan jihar Imo ya lashe zaben fidda gwanin jam'iyyar APC a zaɓen gwamnan da ke tafe a jihar Imo
Gwamna Hope Uzodinma, ɗan takara ɗaya tilo da ya shiga zaben fidda gwanin APC a jihar Imo, ya samu nasara da kuri'u masu rinjaye.
A ranar 11 ga watan Nuwamba, 2023, INEC zata gudanar da zaben gwamna a jihohin Najeriya uku, cikinsu harda jihar Imo.
Asali: Legit.ng