Abin Kunya Har Ina: Shugaban NNPP da ‘Dan Takaran 2023 Sun Barke da Rigima a Fili
- Ana rikici a NNPP a game da wanda zai wakilci jam’iyyar a kotun sauraron korafin zaben Ogun
- Olufemi Oguntoyinbo ya bukaci kotu ta canza Lauyan da ya tsayawa jam’iyyarsa, hakan ya jawo rikici
- Tsohon shugaban Jam’iyyar NNPP, Oginni Olaposi ya ce babu wanda zai iya canza masu Lauya a kotu
Ogun - Sabani ya shiga tsakanin jagororin jam’iyyar NNPP na reshen jihar Ogun, abin da ya jawo hakan shi ne lauyan da za a dauka a kotun zabe.
Rahoton da Punch ta fitar ya fallasa yadda ake rigima tsakanin Olufemi Oguntoyinbo wanda ya yi wa NNPP takarar gwamna da kuma Sunday Oginni.
Sunday Oginni shi ne shugaban jam’iyyar NNPP mai alamar kayan dadi na reshen Jihar Ogun.
Jam’iyyar hamayya ta shigar da kara a kotun sauraron korafin zaben Gwamna da ke zama a Abeokuta, ta na kalubalantar nasarar Dapo Abiodun.
An rasa abin da NNPP take so
NNPP ta na so kotun mai zama a Isabo ta soke galabar da INEC ta ce jam’iyyar APC ta samu.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Ana haka sai aka ji Femi Oguntoyinbo ya je kotun a ranar Juma’a, ya na neman a ba jam’iyyarsa damar canza lauyan da zai wakilce su a shari’ar ta su.
Kotu ta ce a canza Lauya
‘Yan jarida sun ce Alkali ya gamsu da bukatar Oguntoyinbo, ya umarci Peter Ogah wanda shi ne Lauyan da aka yi haya, da ya janye kan shi daga karar.
Da alama korar lauyan na kamfanin Peter Ogah & Partners bai yi wa ‘dan takarar gwamnan dadi ba. Daily Post ta kawo labarin canjin lauyan da aka yi.
NNPP ta bakin Lauyanta, ta ce cire mata suna da aka yi daga cikin takardun kada kuri’a ya saba dokar zabe, don haka ta ke karar har da Hukumar INEC.
Shi kuma tsohon shugaban NNPP na jihar Ogun, Oginni Olaposi ya hakikance a kan cewa sun kai kara a kotun ne saboda ba su gamsu da sakamakon zaben ba.
Olaposi ya ce shi ne wanda ya shigar da kara a kotun zabe da sunan NNPP mai alamar kayan marmari, kuma babu wanda ya isa ya canza masu Lauya.
N2.4m sun komawa PCC
A yau ake jin labarin Kwamitin kamfe ya dawo da wasu kudin yakin zaben Bola Tinubu a takarar 2023 yayin da aka gabatar da rahoton kudin da aka batar.
Prince Ade Omole ya ce kwamitin harkokin kasar waje ya samu N10m ne daga hannun PCC a lokacin yakin neman zabe, amma Naira miliyan 2.4 sun ragu.
Asali: Legit.ng