Yadda Yan 'Obidients' Suka Ceci Peter Obi a Filin Jirgin Saman Landan
- Yan Obidients sun kai wa ubangidansu dan takarar shugaban kasa na jam'iyyar LP, Peter Obi dauki a Landan
- Magoya bayan na Obi sun nemi jin dalilin bata masa lokaci a lokacin da jami'an tsaron Ingila suka tirke shi
- A nan ne jami'an hukumar kula da shige da fice da suka cika da mamaki suka sanar da su cewa ana yi masa tambayoyi ne
London - Daily Trust ta rahoto cewa ba don yan Obidients masu goyon bayan dan takarar shugaban kasa na jam'iyyar Labour Party, sun shiga lamarin ba, da Peter Obi ya shafe karin awanni a tsare.
Da farko mun ji yadda jami'an tsaron kasar Ingila suka tsare Obi kan zargin basaja a filin jirgin saman Heathrow da ke birnin Landan.
Yan Obidient sun ceci Peter Obi a Landan
A cewar kakakin kwamitin yakin neman zaben Obi/Datti, Diran Onifade, an tsare Obi sannan aka yi masa tambayoyi kan wani laifi na rashin gaskiya wanda ke nuna wani na ta yi masa sojan gona a birnin Landan.
DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka
Onifade ya ce martanin yan Najeriya wadanda ake zaton magoya bayan Obi a filin jirgin sama na Heathrow ne ya ceci dan takarar shugaban kasar na LP. A yanzu haka, Obi ya dawo daga Landan inda ya yi bikin Easter.
Ya ce:
"An yi masa tambayoyi na dogon lokaci kuma hakan ya zamo abun mamaki ga mutumin da ya shafe fiye da shekaru 10 a wannan kasar.
"Tunda fuskar Obi ta rigada ta shahara a duniya, musamman a wajen yan Najeriya, yan Afrika a gida da waje wadanda suka kasance yan Obidients, sun gaggauta daga muryoyinsu suna al'ajabin wani dalili ne yasa ake bata masa lokaci.
"Dole jami'an hukumar kula da shige da fice wadanda suka cika da mamakin martanin mutanen suka fito suka bayyana cewa ana yi wa Obi tambayoyi ne kan laifin basaja wanda ke nufin wani na yi masa sojan gona a Landan.
"Babban illar laifin shine cewa ta yiwu mai sojan gonar yana aikata manyan laifuka da ayyukan rashin gaskiya da sunan Obi."
Kotu ta ki ba da belin mai zanga-zangar kin jinin rantsar da Tinubu
A wani labari na daban, mun ji cewa kotu ta hana belin mutumin nan da ya yi zanga-zangar kin jinin rantsar da Bola Tinubu, zababben shugaban kasa a ranar 29 ga wayan Mayu.
Asali: Legit.ng